MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 3 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 3 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 3 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

*_ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ_*

_______________________________

B’ata rai tayi had’e da turo baki, sannan tace “to muga kayan in gani in zan iya sakawa”.

Mik’ewa yayi ya nufi wardrobe ya bude ya d’auko wata bak’ar leda, sannan ya mik’a mata yana mai cewa “amma dai sai kinyi wanka zaki saka ko, tunda na ga rabonki da wanka tun jiya da safe”.

“Haba Usman, wai don Allah baka barina in huta, ka matsa sai na saka maka kaya, kuma kana maganar inyi wanka, please ka kyaleni ” ta karasa magana tana mai waftar ledar kayan daga

hannunsa, samun bakin gado yayi ya zauna yana mai binta da ido, yayin da ita kuma take kiciniyar fito da kayan daga ledar, pencil skirt ne irin mai tsagunnan har sama kalar cofee colour, sai crop top kalar milk, wacce aka k’awata gabanta da wasu irin stones masu sheki, d’aya kayan ta kuma yi a wulak’ance tana mai kallonsa, yayin da shima ya tsareta da ido yana mai karantar yanayinta, watsar da kayan tayi akan gado tana mai fad’in “wai kai Usman wani irin mutum ne ka mai budurwar zuciya, kai wai har yau baka san ka girma ba, wannan kayan ne zan saka, wannan ma ai wulak’ancine da rashin sanin darajata, wannan kayan ai sai su Asma’u ba dai niba, don haka bari in tattara in ajiye mata in ta dawo na bata”, gaba d’aya kasa magana yayi, haka yake binta da ido, yana mamakin halinta na rashin wayewa ta maida kanta wata *_BAGIDAJIYA (HASEENA BAMMALI)_* , ita komai dai na yara ne, ko da yake dama haka *_matar bahaushe_* take, haihuwa d’aya sai kaga sun jeme, su wai sun zama iyaye, haka ya ci gaba da binta da ido yana ta zancen zuci har ta maida kayan leda ta fice dasu a hannu, ganin haka ya saka shi sauke wata k’arfafar ajiyar zuciya sannan ya mik’e ya shiga toilet don yin wanka.

Ko daya gama shiri a parlour ya tarad da ita tana guga, kallo d’aya ya mata ya nufi hanyar barin parlourn, ganin haka yasa ta saurin mik’ewa ta biyosa tana mai cewa “ga abun karyawarka ba naga kuma zaka fice,”, ba tare da juyowa ya kalleta ba yace “bazan ci ba”, cikin rashin damuwa da amsarsa tace ” okay , dama yau ne taron mu fa, kuma gidan hajiya Luba za ayi taron, gashi banda ishashhun k’udi a hannu”.

Fasa fitar yayi ya dawo d’akin tare da cewa “Amina nasha fad’a miki ki fitar da kanki a cikin wannan kungiya, ni ba mai kud’i bane, ko tsaya dai² matsayinki, duk matan nan da kike gani daga matar babbar ‘yan kasuwa, sai na manyan ma’ikatan gwamnati, kinga kuwa wutsiyar rak’umi tayi nesa da k’asa, don haka ki kama kanki, ki tsaya dai² matsayinki”ya karasa magana yana mai nunata da yatsa.

Tun daya fara magana take binsa da wani irim kallom k’ask’anci har sai da yayi shiru sannan ta kada baki, tana mai yamutsa fuska tare da k’ank’ance ido tace “Usman kenan, ai duk wannan zancen naka na sani, saboda dai ni nake cikinsu ni nasan arzikin mazajensu, to bari kaji ba wacce zata nuna mun komai a cikinsu sai dai su nuna muni su hannun mazajensu a bud’e suke, suna musu yayyafin nera, sab’anin ni nawa da baya yi, an fad’a maka bansan me kake ciki bane, Usman kullun nuna wa kake baka da k’ud’i, rufin asirin Allah ne, Alhalin k’arya ne, nice dai baka son yi mini, in ba haka ba ai kana ma yaranka, ko an fad’a maka bansan dubban kud’in da kake biyan musu bane na makaranta, talaka ne zai biya wad’annan kud’in, idan baka dashi kuma ina ka samu k’udin da kaje hajji dashi?”‘

Mamakinta ne ya kamasa tun da ta fara magana har ta gama, numfashi ya sauke sannan yace ” ban tab’a sanin rashin hankalin naki ya kai haka ba sai yau Amina, rufin asirin Allah ne kike k’aryatawa, su kansu manyan masu k’udin ba Allah ne ya rufa musu asirin ba, da kuma kike fad’in zuwana hajji, ai hajji kiran Allah ne, kuma kinsan da yanda na had’a kud’in na tafi, har kina fad’in kece dai bana yi mawa, dame na rage ki Amina?, ci ko sha?, ko sutura?, ki fad’amin wanne be bana miki, suturar da nake miki ma tafi ta yaran, yanxu leshin da kike gogewa 25k na siyan miki shi ke d’aya, amma duk da haka baki gani, any way kanki ake ji, ni dai Allah yana gani ba hakkinki daban sauke miki, sai dai ke kina can kina kallon na sama dake, shi yasa nace miki bansan wannan kungiyar don duk anan kike gano abubuwan da kike saka ma ranki, ki zo ki hana ni kwanciyar hankali, kema ki hana kanki, don haka ya rage naki, in kin gyara kanki, in baki gyara ba ma haka, in lokacin d’aukar mataki yayi zan d’auka, kinga ni tafiyata” nan ya fice ya barta tana ta banbami ita k’adai, yayin da ya gungura mashin d’insa ya bar gidan, jin fitarsa ya sata jan tsaki, tana mai fad’in “wallahi zaka dawo ka sameni, k’ungiya kuma ina nan daram dam, ba zan barta ba”.

Tafe yake, amma gaba daya hankalinsa baya jikinsa,gaba d’aya ya tsunduma duniyar tunani, don Amina ba k’aramin b’ata masa rai tayi ba, ba kalmar da tafi damunsa illa yanda take k’aryata ni’imar da Allah ya masa, anya kuwa Amina kwakwalwarta dai² take, ai wannan kamar izgili take ma ubangiji, gaskiya ya gaji da halinta ya kamata ya d’auki mataki, amma kuma wani irin d’aukar mataki zai yi?, shi dai yasan yana son matarsa ba zai iya sakinta ba, take wani b’angare na zuciyarsa ya bijiro mai ya k’ara aure, amma kuma shi bai da burin haka, a tsarin rayuwarsa yafi son zama da mace d’aya don mutum ne shi da bai son hayaniya da tashin hankali, in ma ya k’ara auren ai baida wurin ajiye matar, sai dai ya kama mata haya, Kuma a yanxu bai da wannan halin, duba da yanda haya tayi tsada, to inma ya k’ara auren, yana da yak’inin wacce zai auro d’in zata kasance dai² da ra’ayinsa?, zata masa biyayya?, don shi gani yake mata duk halinsu d’aya, suna waje ka gansu nagari ga tsafta da kwalliya amma suna shigowa haihu d’aya biyu zata chanza, kwalliyarma sai dai in zasu fita zaka gansu da ita, gaba d’aya kulawar da ake baka zata koma kan yara, kai anya kuwa kar fa yaje ya k’aro ma kansa wata matsalar, shi gashi bai son zancen matsalar gidansa da kowa, balle yaje neman shawara, da ire iren tunanin nan ya k’arasa kasuwa ya bud’e shago, fara shigowar customers yasa shi watsar da tunanin ya shiga ciniki dasu, don Alh Usman kullun shagonsa a cike yake da ‘yan sari da masu siyan d’ai², saboda gaskiyarsa da rik’on amana.

***** *****

Ganin yana ta knocking d’in kofar ba a bashi izinin shiga ba ya sashi bud’e kofar, a tunaninsa ko ya shiga toilet ne, don Secretary dinsa ta sanar dashi yana ciki, zaume yagansa ya dafe hab’a, yayin da ya tsira ma waje d’aya ido, alamun ya lula duniyar tunani, har ya k’arasa wajensa ya ja kujera ya zauna bai masan yayi ba, tsira masa ido yayi tare da nazarinsa, ganin sun d’auki lokaci ba tare da ya dawo hayyacinsa ba, yasa shi buga table d’in dake gabansu da k’arfe, firgigif yayi ya dawo hayyacinsa tare da kai duban sa gareshi yana mai cewa “A’ah, ashe kaine, yaushe ka shigo ne?”.

“Hmm, just some minutes back, na shigo ka lula duniyar tunani, me yayi zafi ne director?”cewar Alhaji salisu yana mai tsaresa da idanu.

Gyara zama yayi hade da sauke ajiyar zuciya yace “AG, wallahi abubuwane sun mini yawa, ga ta office gata gida, ka rasa wanne zaka yi tunani”.

Zaro ido yayi yana mai gyad’a kai tare da cewa” haba dai Director, matsala dai ta office, amma ta gida kuma, kai da kake da mata da kake da mata d’aya, yaran kuma duk suna boarding school, wa zai baka matsala, matsaloli ai sai mu, mata biyu, ga yara bakwai, ai kaga irinmu ya kamata muce haka”.

“AG kenan, ai gwara da kai, tun da dai kana ganinsu a gida, ni tawan ina ma na ganta, yau ta tafi seminar, gobe conference lectures aikin fa kenan bata zama, wani lokacin ma bata country d’in, yanxu haka wata seminar zata je malaysia, bata fad’amin ba sai data shiryo zata wuce, to wannan ba matsala bace, mace bata da lokacinka, hakkinka sai ayi wata ba a baka ba, gyaran d’akinka, abincinka duk masu aikine ke yinsa, yaran kuma da zaka gani su saka ka nishad’i ta kaisu boarding saboda su kansu bata da lokacinsu, mai na rage ta dashi, gaba d’aya ta saka ma kanta neman duniya sai kace wacce ke ciyar da duka danginsu, wallahi na gaji, dama ina so anjima inzo wurinka neman shawara, kuma ina son ka nemo min yarinyar da zan aura, irin taka matar ‘yar sweet 16 dinnan, da zata samamin kwanciyar hankali ” ya karashe magana cikin b’acin rai.

Murmushi mai kama da yak’e Alhaji salisu ya saki, sannan yace “Raba kanka da ‘yan sweet 16 dinnan Director, wad’annan ma sun fo kowa matsaala wallahi, ni kaina ina dana sanin Auransu”.

Fuskarshi dauke da mamako yace ” matsala kuma, wata kalaaaa….”.

*_Toh, ya kuka ga labarin, wake k’alabulanta ta, shin haka matan hausawar suke, ko kuwa ba haka ba?_*

*Sharhinku shine kwarin gwiwa na?*

_*Fateeyzah mbs✍️*_ ¹¹ ¹⁵

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 3 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Kelle Weber

Last Updated:

Views: 5509

Rating: 4.2 / 5 (53 voted)

Reviews: 92% of readers found this page helpful

Author information

Name: Kelle Weber

Birthday: 2000-08-05

Address: 6796 Juan Square, Markfort, MN 58988

Phone: +8215934114615

Job: Hospitality Director

Hobby: tabletop games, Foreign language learning, Leather crafting, Horseback riding, Swimming, Knapping, Handball

Introduction: My name is Kelle Weber, I am a magnificent, enchanting, fair, joyous, light, determined, joyous person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.