MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 4 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)

Kuma Gyara zama Alhaji salisu yayi, sannan yace ” wallahi matsalarsu tafi ta manya, matsala ta farko, ba don Allah zasu aureka ba, haka kuma badon suna sonka ba, face don dukiyarka, haka suma iyayensu don kwad’ayin dukiyarka zasu baka, saboda idan ka lura gaba d’aya auren babu match, kai kana da 54 ka auri ‘yar 16 kaga akwai matsala, na biyu kuma basu da kunya, basu da ladabi, daga ranar da ka had’a gado da kai, ta ganka tsirara, to maganar gaskiya ta gama ganin girmanka sai dai kayi ta hak’uri, kai k’arshe ma zaka fad’a mata magana sai kaji ta k’aryataka( zaro ido director yayi cike da mamaki), gyad’a kai yayi ya ci gaba da yes zata k’aryata ka, ka fad’a mata magana sai kaji tace “Allah!, da gaske!, rantse!” (Kwashewa da dariya

suka yi gaba d’aya) kaga kuwa ta k’aryataka, bata yadda da abunda ka fad’a mata ba, matsala ta uku, bata waye ba, domin tayi rayuwarta daga gida, sai makaranta tare da k’awaye irinta, kai dressing wannan basu iya ba irin na iyayenta zata dinga yi, tunda shi taga ana yi a gidansu, kullun cikin riga da zani, balle kuma aje ga girkin zamani nan zaka sha takaici, kullun daga shinkafa, taliya, dambu, fate da tuwo zaka ringa ci, ba a san a had’a maka drinks ba balle snack, kuma ga kayan had’in ka siya ka ajiye, kai tawa fa dana aureta bata san banbancin da kuma abunda ya kamata a ci for breakfast, lunch, and dinner ba, don wallahi har d’umaman taliya take min da safe in ta ragu,(dariya director yayi) ga shegen bani², yanxi fa k’ud’in kayan miya kullin 1k nake bata, kaga a week 7k kenan, amma abun naira biyar ta siya sai ta tambayeni kud’insa, wanda ni a tunanina in tayi amfani da kayan miya sosai, ta yi amfani dana 2k, 5k ya zama taci riba dani, amma ita kullun baza da kud’i, ga son nuna suna dashi ga ‘yanuwansu da k’awaye, hade’e da iyayin su matan wane ne, wallahi in na tsaya lissafo maka matsalolinsu sai mu kwana a nan, don dai ni nayi degree, don haka kada ka maimaita mistake d’in da nayi, don ni wallahi a yanxu har gwararmun hajiya Luba, don ita tana d’an tarairaya ta”

Gyad’a kai yake fuskarsa d’auke da mamaki yana mai cewa “chab di!, nifa wallahi ganinsu nake na kirki, wad’anda zaka iya juyawa, a kula da kai, a kuma baka soyayyayya wal….”, katseshi yayi ta hanyar fadin ” so me?, ba wata soyayya malam sai dai hak’uri, amma wallahi basu iya soyayya ba balle aje da kula da sauransu”.

“To kai yanxu AG wace irin mace kake ganin zan aura?, wacce zan samu duk soyayya da tarairaya, wacce zata zame mini wife material” cewar director yana tambayar Alhaji salisu.

Mik’ewa yayi tsaye yana mai fadin ” zan fad’a maka later, don yanxu lokaci ya tafi, kuma ina so inje wurin staff officer muyi relocating d’in _*SIWES STUDENT*_ “‘

“Yawwa! dama ina son maka zancen, please kada kh kawo min su office, don na last year banji dad’insu fa, they make me suffered” ya fad’i fuskarsa d’auke da damuwa.

Tsaresa yayi da ido yana mai tambayar ” baka ji dad’insu kamar ya?”.

Shima mik’ewa yayi yana mai bashi amsa da “duk ‘yan college of Education aka had’a mini, and so locals wallah, even good english they can’t speak, ga shi is like basu gane karatun ne, ko rashin maida hankali ne, don har sai dana yi ma supervisor d’insu k’orafi da yazo, nan ma cemin yayi yawancinsu haka suke, suma haka suke fama dasu, kuma already dama kasan matan garin nan, basu wani waye ba”.

Dariya Alhaji salisu yayi yana mai fad’in ” kace ka ci wuya, but kaima kasan a garin nan, yaushe ma suka fara barin yaransu na karatu, yawanci daga secondary sai aure, wasu ma basu k’arasawa, kuma kaga secondary d’in ma ba wani mai da hankali suke yi ba, don in da suna mai dawa, wallahi wani d’an secondary d’in ya mafi d’an jami’ar k’warewa da turancin, nan fa da kake ganinsu yaran manyan garinne, kaima kasan in ba don haka ba , baza a k’arbesu ba a nan, maganar wayewa kuma wannan daga gidane, da kuma yanayin garin, shi yasa ni fa in zan k’ara aure kaduna state kawai zan tafi in zab’o mata, kasan ko k’auye kaduna ne, yafi k’auyen ko wani state, ga wayewa, ga ilimi but addini dana boko”

*_(Sorry hoo, dole in k’od’a state d’ina, kaduna crock city, kaduna garin gwamna, kaduna cibiyar arewa, kaduna birnin ilimi, ?‍♀️nayi nan, kar inji bugu)_*

Dariya Director yayi tare da fad’in “wai kai a yanxu har wani aure zaka kuma k’arawa bayan mata biyub da kake dasu, haba AG, ai mu ya kamata mu k’ara”.

“Hmmm, kaji kadai, indai na samu wacce tamin wallahi k’arawa zanyi, ba gashi *ICT DIRECTOR* zai k’ara ta uku wannan satin ba”cewar Alhaji Salisu yana murmushi.

“Wallahi fa haka naji, anma ce wai wata yarinya da tayi IT last year zai aura ko?” Director ya k’arasa maganarsa had’e da tambaya yana tsaresa da ido.

Da mamaki d’auke da fuska yace “haka ne wallahi, yarinyar ma ai a office d’ina tayi IT, tana karatu anan d’an fodio university sokoto”.

“Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi, ya nuna na ‘yan baya” cewar director yana zama kan kujerarsa.

Nufar k’ofa yayi yana mai fad’in “Amin ya Allah, ni na tafi, sai mun had’u”.

Amsawa yayi da “ok”.

****** ******

Zaune suke a babban parlourn suna ta hira, ‘yan k’ungiya kenan, da suke taro a gidan hajiya Luba, wanda suke su Shidda ne ,Hajiya Amina matar Alhaji Usman, sai Hajiya Aisha mijinta professor ne a jam’ar tarayya dake jahar, sai Hajiya Atine, mijinta babban d’an kasuwa ne da yayi suna a jahar, sai Hajiya Turai, ita kuma mijinta shine commissioner noma, sai Hajiya Sailuba, itama mijinta d’an kasuwa ne, sai Hajiya Luba da take kitchen ita ce cikon ta shiddansu.

Sallama Lawal Almajiri yayi a bakin k’ofar parlourn, nan suka amsa masa, wanda yayi dai² da fitowar Hajiya Luba daga kitchen tana mai Cewa “Lawal shigo mana”, shigowa yayi yana mao gaishesu, yayin da suka amsa masa a wulak’ance tare da shan k’amshi.

“Hajiya Atine don Allah duba min kujerar da kike zaune na ajiye k’udin cefanen da Daddy ya bani d’azu” cewar Hajiya Luba.

Muskud’awa Hajiya Atine tayi , ta zaro kud’in tana mai cewa ” nakuwa gani sanda zan zauna, dubu biyu(2k) ko?”ta karashe zancenta tana mai zaro kud’in ta mik’a mata.

K’arfa tayi tana mai cewa ” aikuwa sune na gode”, sannan ta fuskanci lawal ta mik’a masa tare da cewa ” gashi nan ka siyo mini kayan miya, tumatir, tattasai, tarugu, albasa na dubu biyun(2k), sai kuma ga wannan dubu biyun (2k) (ta ciro a aljihun doguwar rigarta ta mik’a masa), ka siyo min ganda (kpomo) na dubu d’aya (1k), sai had’in su green beans na d’ari biyar (500), da had’in ganye shima na d’ari biyar(500), sai kace ma maigadi ya ara maka kekensa kaje a kai”.

Amsawa yayi cikin ladabi ya fita, hajiya Aisha ce ta bud’e baki cike da mamaki tana mao cewa ” Hajiya Luba, cefanen ne har na dubu hud’u (4k) bacin shi dubu biyu (2k) ya baki, maimakon ki rage, naga kin k’ara ma da naki kud’in”

Hajiya Ameena ce ta cabke da cewa “nima dai abunda ya bani mamaki kenan, mu dama ake bamu bai kai haka ba, muna ragewa ballanta ita, wannan ma ai ba riba sai fad’uwa”.

K’ayataccen murmushi Hajiya Luba ta saki tana mai cewa ” a ganinku ne bana cin riba, ni kuwa nasan ribar da nake ci babu mai ci a cikinku, wannan cefanen da kuke gani, in kuka cire ganda cefanen sati d’aya kenan nayi, a kullun Daddy dubu biyu (2k) yake bani na cefane wanda inkin had’a na sati d’aya yana bani 14k kenan,duka cefanen da nake yi a sati dubu hud’u nake kashewa, domin in kun cire abubuwan danace lawal ya siyomin bana siyan komai, domin kuwa Daddy yana ajiye komai, kunga kuwa nike cin riba, tunda duk sati ina tashi da 10k, wanda ko business din dana ke iyakarta kenan”

“Lalle kam, ke dai kin cab’a, Amaryaki fa ita kuma nawa ake bata?” Cewar Hajiya Amina cike da son jin gulma.

Hajiya Sailuba ne ta cabke da cewa “Haba dai Hajiya Amina, kema dai kinsan Amarya ta wuce nan, kamar kin manta halin mazan yanxu na rashin adalci”

Mumushi hajiya Luba tayi mai kama da yak’e tace ” wannan kuma ban sani ba, kuma ban damu da in sani ba, tunda dai ni yana sauke hakk’ina dana ‘ya’yana akansa, in ma dubu d’ari (100k) zai ringa bata ba matsalata bace, nasan dai in zai shekara yana bata, baza ta tab’a cin k’udinsa ba yanda ni naci, kada fa ku manta shekaranmu 25 tare, ita kuwa duka² shekararta biyu a gidansa”.

Shewa suka d’auka gaba d’aya suna mai fad’in “yayi uwargida ran gida, shi yasa kike sha’aninki”.

Fari tayi da ido tana mai cewa ” ya san ranku, nifa in Daddy zai wata bai bani kud’in cefane ba bazan tambayesa ba, kuma zan dafa in basa, cima kuma baza ta canza ba, don dai Allah kad’ai yasan nawa na samu a jikinsa”.

Tab’e baki hajiya Amina tayi tana mai cewa ” sannu dad’i miji, wallahi ni indai baka kawo ba, wallahi bazan dafa in baka ba, sai dai in dafa ni da yarana mu cinye, don su kad’ai ne bazan iya hana su abinci ba,shi kuwa duk samun da nake a jikinsa in bai kawo ba, nima bazan daga ba…”

“Kice ki kina da babban aiki wallahi, gwara ma tun wuri ko canza” cewar Hajiya Luba.

Gyaran murya Hajiya Turai tayi tare da cewa “aikam, ni bama wannan ba, ni fa ina da matsala, Alhajine zai k’ara aure, shine nake neman shawararku, don wallahi so nake in wargaza auren, don bazan iya zama da kishiya baa….

*_Tofa, chakwakiya, matar bahaushe kenan, ko ya zata kaya._*

*_Fateeyzah mbs✍️_* ¹⁶ ²⁰

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 4 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Mrs. Angelic Larkin

Last Updated:

Views: 5497

Rating: 4.7 / 5 (47 voted)

Reviews: 86% of readers found this page helpful

Author information

Name: Mrs. Angelic Larkin

Birthday: 1992-06-28

Address: Apt. 413 8275 Mueller Overpass, South Magnolia, IA 99527-6023

Phone: +6824704719725

Job: District Real-Estate Facilitator

Hobby: Letterboxing, Vacation, Poi, Homebrewing, Mountain biking, Slacklining, Cabaret

Introduction: My name is Mrs. Angelic Larkin, I am a cute, charming, funny, determined, inexpensive, joyous, cheerful person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.