MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 5 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 5 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 5 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

Gaba d’aya ido suka zuba mata, yayin da zukatansu ke ayyana abubuwa daban² har zuwa lokacin data dasa aya a maganarta.

Hajiya Aisha ce ta yanke shirun tare da cewa ” tashin hankali wanda ba a sa masa rana, wai me ke damun mazan mune na hausawa, su dai basu da magana sai ta k’ara aure, auren ma sai sun ga ka manyanta yara duk sun girma, gaskiya da sake wannan al’amarin, shi kinsan aure kamar kiranye ne, da zaran mutum d’aya ya fara sai kiga sauran ma sun yi, ballantana mu da aka saka mana ido a garin nan, gaskiya ya kamata mu d’auki mataki tun wuri kafin abun yazo yafi k’arfin mu”.

Gaba d’ayansu in ka cire Hajiya Luba gyad’a kai suke alamun sun yi na’am da zancen Hajiya Aisha.

“To wani irin mataki kuke ganin zamu d’auka, don ni ma kaina gaskiya abun ya fara bani tsoro, wallahi yanda na tsani mutuwata haka na tsani inji zancen kishiya” cewar hajiya Atine fuskarta d’auke da b’acin rai.

Dariya Hajiya Turai tayi mai kama da yak’e, sannan tace “Hajiya Atine naki da sauk’i, nifa sunan kishiya ne bana k’aunar jinsa, wallahi ko labari naji an ma wata kishiya bana iya bacci, nifa yanda na tsara rayuwata babu maganar kishiya, yanda na taso naga uwata ita kad’ai a wurin babana haka nake son nima in kasance a wurin mijina, kai hatta ‘ya’yana su kad’ai nake da muradin gani a wurin mazajensu, shine kuma ni yanxu xa’ace za a mun, wallahi nayi alk’awarin ko meye zanyi duk wahalarsa indai zan tarwatsa maganar auren nan na Alhaji”.

“To yanxu meye abunyi tunda dai kunga tun kafuwar k’ungiyar nan tamu ta *MANYAN MATA* , wannan ne first incidents d’in da ya faru da d’ayanmu tunda kunga already ita Hajiya Luba ko da muka kafa k’ungiyar nan da tata kishiyar, kunga wannan sai mu iya cewa shine na farko, don haka meye solution?” Cewar Hajiya Amina tana mai mik’ewa tsaye.

Hajiya Sailuba da tun farko B’acin rai ya hanata magana ne ta sauke wata k’afaffiyar Ajiyar Zuciya , cikin bacin rai had’e da zafin kishi tace ” solution kenan mu dakatar da auren nan ta k’arfi da yaji, ke naki aikin Hajiya Turai shine ki hana sa kwanciyar Hankali, bala’in safe daban, na rana daban, na dare ma daban, sannan yara ma ki zuga su suyi masa bore, kunga idan kuka yi haka kun dasa masa rashin kwanciyar hankali, mu kuma kibar mu da ita amarya, zamu je har gida muyi mata concrete warning, sannan mu tsoratata ta yanda da kanta zata ce bazaa ta auresa ba, haka ma iyayenta, mu samu mu masa sharri a wajensu, kinga ta haka ne zasu janye, kinga muyi maganin matsalar kenan, ko ba haka ba *MANYAN MATA* “.

Dukkansu amsawa suka yi da “hakane wallahi” in ka cire Hajiya Luba data zuba musu ido tana mai mamakin k’awayen nata.

Idonta jajir ta amsa musu da “nifa ban san gidansu ba, hasalima bansan sunan yarinyar ba, don ni tun ranar da ya fad’a mini ban bari ya kuma wata magana ba na masa tijara har na gaji sannan na bashi waje, to ban kuma bari mun had’u bama, shima kuma bai kuma mun magana ba, don irin borin dana masa daga gani ya tsorata”.

Tsaki hajiya Aisha taja “mtseewww” tare da cewa ” kin jiki kuma, ai dole yanxu kibi hanyar da duk zaki bi ki binciko mana ita, don mu samu mu aiwatar da Aikun mu kafin lokaci ya k’ure mana, ba boka ba malam, amma kawai makamanmu da tuggun mu ya isheta ita da iyayenta”.

Gaba d’ayansu suka kwashe da dariya yayin da Hajiya Luba ta girgiza kai tana mani tab’e baki.

Hajiya Atine ce ta Kalli Hajiya Luba tana mai cewa “Hajiya naga ke tunda aka fara maganarnan bakk saka baki ba, sai binmu kike da idanu, kuma ke ya kamata ma muji ta bakinki tunda dai ke an d’ana miki kinji”

“Hmmm, to ai ni mamaki kuka bani wallahi, akan kishiya kun maida wurin nan kamar filin yak’i, me aka yi aka yi kishiyar?, k’aramin Alhaki, ko da yake ni kaina nayi wannan haukar da tijarar, amma daga baya Allah ya nuna mini wata hanyar, sai gashi a k’arshe yayi aure, ba abunda na ragu, sai ma k’aruwa, ita kanta kishiyar tasan na mata fintink’au nafi k’arfinta, shi yasa har yanxu ina ganin babu macen da zata zo ta wuce ni, duk tsiya sai dai tabi bayana, shi yasa kawai na biku da idanu” tayi magana cike da Alfahari.

Gaba d’aya zubo mata ido suka yi tare da had’in baki wurin cewa ” wace hanya ce?, fad’a mana don Allah”.

Murmushi tayi sannan ta fara da cewa

*_Fateeyzah mbs✍️_*²¹ ²⁵

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 5 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Aron Pacocha

Last Updated:

Views: 5499

Rating: 4.8 / 5 (48 voted)

Reviews: 87% of readers found this page helpful

Author information

Name: Aron Pacocha

Birthday: 1999-08-12

Address: 3808 Moen Corner, Gorczanyport, FL 67364-2074

Phone: +393457723392

Job: Retail Consultant

Hobby: Jewelry making, Cooking, Gaming, Reading, Juggling, Cabaret, Origami

Introduction: My name is Aron Pacocha, I am a happy, tasty, innocent, proud, talented, courageous, magnificent person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.