MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

Murmushi tayi sannan ta fara da cewa “A lokacin da Daddy yazo min da mganar zai k’ara aure,ba k’aramin bori na masa ba, ke har ta kai ya dena kwana a gidan nan saboda ni, saboda rashin mutunci ba wanda ban masa ba, yara kuma abu k’ad’an zasu yi in hantaresu, amma duk abunnan danake yi bai hanasa ci gaba da shirye shiryensa ba, ni kuma kullun da sabon tijarar da zan masa, ranar kawai naji ina marmarin hawa Facebook, don rabon da inyi wani chat tun ran da Daddy ya sanarmin da maganar k’arin aurensa, ina shiga naci karo da post din *Fateema Zahra Muhammad sani(Fateeyzah mbs)* admin ta group din *A Turakar mijina* da kuma *Sirrin Turakar miji*, wallahi post d’in kamar don ni tayi sa, wanda take magana akan haukan da uwargida take yi in maigida yace zai k’ara aure, sannan da shawarwari da ta bada, wallahi ina

karantawa naji na muzanta, jikina yayi sanyi, hakan yasa nabi ta private, sai dai bata min reply ba, hatta friend request d’in dana tura mata bata yi accepting ba, nan hankalina ya kuma tashi, na kuma bin ta post d’inta na mata magana, nan ma bata min reply ba, sai dai sauran members da suka min reply da inyi hak’uri zata amsa ni, mutane ne ke mata yawa, sai da nayi sati d’aya da mata magana sannan tayi attending d’ina, inda na mata introducing kaina tare da karanto mata matsalolina, wallahi cikin 20minutes ta bani shawarwarin da har yanxu akansa nake, wato inyi hak’uri, in danne kishina, in kuma mik’a lamurana ga ubangiji, nan ta ce in duba group d’in in bincika duka posts d’inta zanga sauran bayani, da shawarwarinta da lectures d’inta nake amfani, shiyasa kullun nake addu’a Alherin Allah ya kai mata a duk inda take”.nan ta tsagaita tana mai binsu da ido

Ganin ba wanda yayi magana yasa ta ci gaba da cewa ” a ranar na tura ma Daddy text message na bada hak’uri, sannan da ya dawo ma na bisa d’aki na zuk’unna har k’asa na kuma basa hak’uri, wannan duk shawarar fateeyzah ne, wallahi a ranar farin cikin gidan nan ya dawo haka muka wuni muka kwana cikin walwala, hidimar bikin gaba d’aya ya dawo da ita hannuna, sannan ganin na kwantar da hankalina yasa ya siyan mata wanu gidan ya fasa ajiyeta a d’ayan part d’in gidannan, haka ya canza mana furnitures mu da yara, sannan ya bani mak’udan kud’i yace inje in had’o ma amaryarsa lefe, nan kishina ya motsa, na tafi da niyyar siyo mata kaya masu arha, marasa quality, sai dai anan na tuna da shawarar fateeyzah da tace in tsayar da gaskiya ta, haka ko na daure na zab’ar mata kaya masu kyau da tsada, sannan akwati na siyan mata set 2, komai dozen na saka mata, daga Atampa, lace, shadda, materials, abayoyi, takalma, jakunkuna, hatta sark’ok’i, sannan na saka mata gwal set biyu, guda full set, guda half set, sai kayan shafa, da inners masu tsada, haka nayo uban kaya na dawo dasu gida, ashe duk siyayyar da nake Daddy ya saka wani yana watching d’ina, na dawo bai fi da awa d’aya ba, sai gashi shima ya dawo da uban kaya , dana bud’e babu abunda ya banbanta da wanda na siyan ma amarya, sai dai banbancin colour, nan yake cemin nawa laifen ne, a lokacin na kumq godiya ga Allah, da na mata mugunta da shikenan nima shi zai kwaso mini, in tak’aita muku a wannan bikin ba k’aramun alheri na samu ba, don a lokacinne ya siyan mini babbar mota, duk mai yajo haka?, saboda na kwantar da kai, ko da aka kawo amarya bai canza min ba, sai ma dad’a kyautatamin da yake yi, amarya tsakanina da ita kuma sai gaisuwa da ganin girman juna, inkin ga tazo sai in wani abune ya faru kamar rashin lafiya, haka nima, ko kuma mun had’u a sha’anin dangin miji, sanna kuma in ba gidanki miji yake ba, baki isa ki kirasa ba, sai dai inshi ya kiraki, wannan kuma duk dokar Daddy ne, shiya sa wallahi ni wani zubin nake mantawa ma ina da kishiya, don sai inyi watanni ma ban ganta ba, don haka Hajiya Turai shawarata gareki itace kiyi hak’uri, kinga dai shi auren nan ibadane, kuma Allah shi ya umurcesu da su auri har hud’u in suna da hali, kinga niyyar dakatawa kamar isgiline “.

“Hajiya Luba kenan, gaskiya a shawarki babu wacce zan iya d’auka balle har inbi, ke in kin had’u da kishiya ta kwarai to ki sani in ba dole bane in had’u da ita, a irin ‘yan matan zamanin nan da suke kokarin raba mata da mijinta tun kafin su shigo, burinsu kawai u fitar data gidan, sannan kuma ke Allah ya had’aki da miji mai nagarta, to ni ba hakan bane, don Alhajina ina ni d’aya ma ya aka k’are balle ya k’aro wata, kuma ko a cikin ‘ya’ya ya iya nuna banbanci balle matansa, don haka ku barni kawai in d’auki mataki” cewar hajiya Turai cikin b’acin rai.

Gaba d’ayansu suka goya ma hajiya Turai baya, inda kowacce ta ci gaba da kawo baragurbiyar shawara, ganin haka yasa hajiya Luba ta nifi kitchen ta basu wuri.

****** ******

Gidan hadiza da malam Ayuba na koma, in da na tarad da ita tana ta faman kasa shinkafar data dafa a kwanuka, kallo d’aya zaka ma shinkafar ka lak’a mata suna da ci karka mutu, haka ta gama kasa abinci sannan ta kira yaran da dawowarsu kenan daga makaranta suka d’auka suka nufi d’aki, bubkasonta da ta iba shi ta zuba ma almajirinta a robarsa saboda babu ragowa, haka ta tashi ta shige d’aki inda ta tarad da yaran suna zaune suna cin abinci, kallon Abdullahi tayi tare da cewa “Abdullahi kayi ka gma kazo ka siyo mini fura in dama da nonon can da malam ya kawo mini don insha magani”.

Kallonta yayi had’e da cewa ” umma fura kuma, baga abinci nan ba”.

Murmushi tayi mai kama da yak’e tace ” eh fura Abdullahi, abincin bazai kai bane, nawa na zuba ma Rabi’u Almajiri”.

Jin abunda tace yasa shi cire hannunsa a nasa kwanon ya tura mata gabanta yana mai fad’in ” umma ga nawa kici, da safe ma fa ina ganin kika juye mana kokon ke baki sha ba, yanxu ma ki zauna da yunwa, ina fura zata d’aukeki”.

Jin hakan yasa sauran yaran suma suka taho wurinta da kwanon abincin a hannu suna masu fad’in ” umma ga namu kici”.

Ganin abunda sukayi yasa zuciyarta tsinkewa, kallonsi take yi cike da tausayi, yayin da hawaye ke bin fuskarta, nawwara ce takai hannu tana share mata hawaye tare da cewa “umma ki dena kuka, kiyi hak’uri”, yayin da Nasmah itama ta rungumeta ta saka kuka, ganin haka yasa hadita share hawaye tana lallashinta, sai da taga tayi shiru, sannan tasaka Abdullahi d’auko babban faranti ta juye dukka abincinsu a ciki, nan duk suka sa hannu suka fara ci har da hadiza wanda take ci k’adan², ganin haka yasa Abubakar cika hannunsa ya kai bakinta, bata da mafita ta bud’e bakin ya saka mata, nan suma sauran suka ciko hannun suna bata, ganin hakan yasa ta dakatar dasu, tace zata ringa ci da yawa, sai gashi Allah ya sa mana Abincin Albarka har sai da suka rage.

*Abu sadiq Islamic medicine store* na nufa, inda na tarad da malam Ayuba da wata had’add’iyar kula a gabansa yana cin abinci, shinkafa da miya ne da wake, ga cinyar kaza a sama da coslow, gefensa kuma kwallin madara hollandia ne yana had’awa da ita.

Malam Ayuba shine mai shagon, kuma Allah ya bashi kasuwa saboda maganinsa na aiki sosai, nan zaka ga mata da maza suna parking da motoci, ga kuma masu mashina, ga masu kuma sayyada, sai dai duk samun da yake baya iya kashe ma iyalinsa, daga cimarsu har suturarsu masu arha ne, makaranta ne kad’ai yake biya ma yaransa, acewarsa saboda yana so in sun kammala su samu aikin da zasu yi kud’i dashi sosai, matan kuma su auri ‘yan boko masu kud’i, haka kullun take kasancewa daga abincin safensa har na dare lafiyayye yake ci a waje, yayin da yabar na gidan da ci kada ka mutu, sai dai kullun alk’awarine in zai shigo da daddare sai ya shigo ma Hadiza da kayan marmari, dasu madara da zuma da magungunan mata, haka zai tsareta sai tasha saboda acewarsa gyaran fadarsa yake yi, wannan ‘yar cimmar yasa ba kowa yake gane hallin da hadizar ke ciki ba, don baya nunawa a jikinta, kullun tsaf zaki ganta, domin hadiza mace ce mai tsafta.

****** ******

Gidan maryam amaryar Alhaji salisu na nufa, inda na tarad da ita zaune da wata mata wacce akalla zata kai shekara 50 a duniya.

Kallon maryam matar tayi tare da fad’in ” maryama yau babu abun tab’awa ne a gidan naki, naga baki kawo mun d’an farfesun nan bane da dan lemun roba”.

Turo baki maryam tayi tana mai cewa ” kai mama, wai ke kullun abunda yake kawoki gidannan kenan, to ni nama na ya k’are, yace zai aiko dashi, lemun roba kuma shima ya k’are, ban ma fad’a masa ba.

B’ata rai mama tayi tana mai cewa ” to maryam in banzo naci a wurinki ba ina zanci, yanxu dai tunda babu naman, ki d’an had’a min tea da kauri, sai ki d’an soya kin kwai”.

Tashi tayi ba tare da ta tankata ba ta nufi kitchen, cikin k’ank’anin lokaci ta had’o mata tea a k’aton kofi tare da sink’in biredi ta dire mata a gabanta tana mai fadin “ga dai abunda ya samu, son kwan ma jiya da k’awayena suja zo na soye musu, dama ragowar kenan guda goma, na soya musu bakwai, yau kuma da safe na soya ma mai gidan uku”.

“Hmmm, kice dai yau nazo da rashin sa’a” tayi magana tana mai kai kofin tea baki, cikin k’ank’anin lokaci ta shanye tea tas, yayin da ragowar biredin ta tura a jaka tana mai cewa ” wannan kuma bari in kaima k’anninki ragowa”.

Kallo kawai maryam ke binza dashi, domin ita dai mamar tata ta fara isar ta wallahi, ita kenan ko da yaushe tana mata sintiri a cikin gida.

Gyara zama tayi tare da cewa ” maryam yau dalilin zuwana shine , babankine zai je kaduna d’aurin aure, to gaba d’aya kayansa sun yi taushi, shine nazo a cikin kayan Alhaji ki bashi koda kala biyune wanda zai samu ya saka”…..

Zaro ido maryam tayi tare da cewa……

*Chakwakiya* ?

*_Fateeyzah mbs✍️_*

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 6 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Horacio Brakus JD

Last Updated:

Views: 5505

Rating: 4 / 5 (51 voted)

Reviews: 90% of readers found this page helpful

Author information

Name: Horacio Brakus JD

Birthday: 1999-08-21

Address: Apt. 524 43384 Minnie Prairie, South Edda, MA 62804

Phone: +5931039998219

Job: Sales Strategist

Hobby: Sculling, Kitesurfing, Orienteering, Painting, Computer programming, Creative writing, Scuba diving

Introduction: My name is Horacio Brakus JD, I am a lively, splendid, jolly, vivacious, vast, cheerful, agreeable person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.