MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

Zaro ido maryam tayi tare da cewa “kayansa kuma mama, haba dai, yanxu idan yazo bai gani bafa, ince masa me?”.

Tsaki mama tayi sannan tace ” tafi can!, wawiya kawai, irin su Alhaji ina suka san kan kayansu, ke hatta kud’i irinsu basu san nawa suka tara ba, baki ganin kashesu kawai suke yi, balle kuma kaya, ko kin d’auka bazai gane kin d’auka ba, don haka umurni nake baki tashi ki d’auko mun, tunda ke baki da kishin kai, kinfi son ubanki ya tafi a tsiyace, ana nuna sa a taro, ana d’iyarsa na auran mai kud’i amma bai canza ba, jiya iyau, yana yawo a tsumma”.

Tashi tayi ta nufi bedroom tana mai zunb’uro baki had’e da gunguni, yayin da mama ke binta da harara tana mai cewa ” jibeta don Allah, wato ke so kike kici arzikin ke d’aya mu kibarmu cikin wahala, to wallahi baki isa ba, hatta k’anwarki data miki hanyar samun Alhaji baki san kiyi mata d’an ihisani ba” ta fad’i dai² maryam na fitowa daga d’aki, hannunta d’auke da sababbin shadda a goge, mik’a ma mama tayi tana mai fad’in ” gashinan kala biyu ne, amma don Allah wannan ya zama na k’arshe mama, don gaskiya abun naku yana yawa, Alhaji na muku, nima ina muku dai² gwargwado amma baku gani, wallahi duk da Alhaji baya nunawa, amma nasan ya fara gajiya da d’auke² da ake masa a gidannan, ga kuma yawan sintiri da kuke, ke kizo, kuma ki turo min yara suma suzo, wannan da gidanmu d’aya da kishiya da nasha gori, don haka na gaji wallahi”.

Baki mama ta bud’e alamun mamaki tana mai fad’in “ehhhhh!, lallai maryam wuyanki ya isa yanka, wato kin manta cikin talaucin da kika fito, ke yanxu kin samu duniya shine kike so ki manta damu, to wallahi baki isa ba, don mun aura miki Alhajine domin mu kanmu mu huta, in ba don haka ba, ai baki kai shekarun aurensa ba, mutumin da ‘yarsa ma ta girme miki, to wallahi da sake, in zaki saki jiki ki saka wayo ki wawusho mana arziki ki saki, in ba haka zan d’aga miki nono wallahi”.

Kallon mama tayi cike da mamaki tana mai fad’in ” saboda haka kike so ki d’aga mini nono, to ai shikenan, wallahi sai in kashe auren kowa ya rasa, in yaso sai abi wani yariman a sha kid’a”, ta karashe magana tana mai yatsina fuska hade da watsa ma mama wani banzan kallo.

” haba mairamu na, daga wasa zaki maida abu babba, ina ni ina d’aga ma shalelena nono, don Allah kiyi hak’uri kada ki kashe auren nan, don inkin kashe mun shiga uku, insha Allah zamu dena miki sintiri a gida, amma dai don Allah ki d’an ringa mana aiken kayan abincin da d’an kud’in akan lokaci” cewar mama cike da lalllashi.

Cikim k’osawa da maganar tace ” to naji, yanxu dai ki tashi ki tafi don Allah”.

Amsawa tayi da “toh ‘yar Albarka, amma ai baki gama sallamata ba, tunda baki bada kud’in mota ba”.

Kallon mama maryam tayi cike da takaici, sannan ta mik’e ta nufi d’aki, d’an kwalin lipton d’in da mama ta hanga kan dinning ta tashi ta d’auko da sauri ta saka cikin jaka, dai² nan maryam ta dawo da dubu biyu a hanu ta mik’a mata had’e da fad’in ” gashinan ku lallab’a dashi har wani satin, don dai wallahi banda kud’i”.

Amshewa mama tayi tana yak’e baki tare da cewa ” toh ‘yar albarka, ai babu damuwa, yanxu dai saura kud’in motar babanki na tafiya kaduna”‘

A fusace ta ce ” banda shi mama, haba abun ai yayi yawa, dole ne wai sai yaje?”.

Cikin rawar baki tace “ba dole bane ‘yarnan, amma dai ya kamata yaje”

Mik’ewa tayi tana fad’in ” to ai shikenan, kwasan yanda zakuyi wallahi, inkin tafi ki kullo mini k’ofa, Allah ya kiyaye hanya” ta fad’i tana mai shigewa bedroom d’inta.

Binta da kallo mama tayi baki a bud’e, sannan tace “ah lallai!, mairamu kin rik’a, to ai shikenan, idan baki bada ba, ma kira Alhajin shi ya bamu, sakaryar banza kawai, ai zaki shiga matsala zaki zo neman shawara” mik’ewa tayi ta fice a d’akin had’e da bugo k’ofa da k’arfi, yayin da maryam ke ta dariya, don ta gama jin duk abunda tace.

*********** **********

Sai wurin k’arfe biyar manyan mata suka watse, inda suka tafi akan jiran bayanai dangane da b’angaren Amaryar da commissioner mijin Hajiya Turai zai yi , yayin da can kuma b’angaren Hajiya Luba take ta gyaran gida ita da yaranta, domin taran Alhaji( daddy).

Gab da magriba Hajiya Amina ta shiga gida, inda tana shiga taci karo da uban wanke² a bakin fanfo, k’wafa tayi tare da fad’in lallai yarannan za kuci ubanku wallahi, wanke² tun na jiya ” ta fad’i tana mai k’arasa shiga cikin gidan.

Shiga d’akin tayi tana mai k’wala ma Asma’u kira, da sauri ta fito daga kitchen hannunta rik’e da ludayi tana mai cewa “umma kin dawo, sannu da zuwa”, amsawa tayi da “yawwa, ya akayi naga wanke² ba ayi ba?”

“Umma ai aikin Munnira ne, kuma tun da muka dawo makaranta taci abinci ta shirya ta fita wai zata birthday bata dawo ba” cewar Asma’u tana mai komawa kitchen don jin k’auri.

K’wafa tayi tana mai fad’in “zata dawo ta same ni wallahi, zata fad’a min uban wa ta tambaya zuwa wani birthday, to ina su kuma su Abdullahi da autana?”

Daga cikin kitchen ta amsa mata da ” su kuma sun tafi filin ball”, kitchen din Hajiya Amina ta nufa tana mai k’ara tambayarta da “me kike dafawa ne” ta k’arasa tana mai bud’e tukunya, sannan tace “au shinkafa da wake, toh da miya ko?”

“A’ah umma da mai da yaji da salad zanyi” cewar Asma’u cike da shagwaba,rufe tukunyar umma tayi tana mai fad’in ” kinsan dai Abbanku baya ci ko, to ke kika sani tsakaninkune” ta k’arashe zancenta tana mai fita daga kitchen d’in.

nufar bedroom tayi wanda yake kacha², don yanda suka barsa jiya haka yake, kallon d’aki tayi cike da takaici, sannan ta kalli agogo k’arfe shidda har da minti biyu, kwab’e kayanta tayi cikin sauri tana mai fad’in “wai!, lokacin film dinnan fa ya kusa ina nan tsaye, duba kayan wankin kan gado tayi ta dauko wata yamutsatssiyar doguwar rigar material ta zura, sannan ta yayime d’ankwalin wata jar atamfa ta d’aura tana mai ficewa daga d’akin zuwa parlour, d’aukar remote tayi ta kamo tashar da take so, wanda har an fara series film d’in, gaba d’aya ta maida hankalinta kan Tvn tana kallo, dai² nan munnira ta shigo d’akin da sallama, ganin ummanta a zaune yasa gabanta fad’uwa, kallo d’aya hajiya Amina ta mata ta maida idonta kan tv, tana mai cewa ” sannunki da dawowa, kiyi maza kije kimin wanke² kafin ranki ya b’aci”.

Cikin sauri munnira ta shige d’akinsu, tana mai jin dad’in fad’an da ummanta bata mata ba, na fita da kuma dressing d’in da tayi na riga da wando, sai d’an mayafi, cire kayan ta fara yi, yayin da Asma’u ta shigo tana maI cewa ” ‘yan birthday, ai ina saurarenki ke da umma a kitchen, wallahi Allah ya taimakeki ne kawai tana kallon wannan series d’in, wallahi da yau taci ubanki don ta d’au zafi akanki da ta dawo baki nan”.

“Gaskiya kam Allah ya taimakeni, ni wallahi ban d’auka ma zata dawo da wuri bane, naga indai suka tafi wannan meeting d’in nasu sai bayan magariba take dawowa” cewar munnira tana k’ok’arin cire riga.

Dariya Asma’u tayi sannan tace “nima wallahi ban d’auka zata dawo da wuri ba, yanxu dai ina kayan birthday”.

Nuna mata jaka munnira tayi da yatsa tana mai cewa “suna ciki, bari inje inyi wanke in na dawo sai muci”.

Amsawa Asmau tayi da “toh” ta fice a d’akin, nan ita ma munniran ta fice, d’akin nabi da kallo, yasha furnitures pink colour amma babu gyara, duk sun zubar da kaya a k’asa, gado babu shimfid’a, ga littattafansu da uniform duk akan gadon.

Itako hakimar tana zaune gaban Tv, har akayi kiran salla aka idar bata da niyar tashi, suma nan yaran suka yi joining d’inta a parlourn suka tasa tv a gaba, sai da aka gama film d’in sannan suka zuzzubo abinci aka hau ci, a tak’aice dai sai da aka kira sallar isha’i sannan ta umurcesu da su tashi suyi salla, yayin da itama ta d’auro alwala ta fara tata sallar, don hatta la’asar bata yi ba, suna can suna chapter.

_Allah shi kiyashemu tab’ewa_

Gaba d’aya titin ya cunkushe saboda go slow, duk da kawai traffic amma bai hana wurin cunkushewa ba, duba da lokacin, wanda dama duk wani magidancin kirki da yasan darajar kansa da anyi sallar isha’i zai nufi gida cikin iyali, da kad’an² go slown yayi sauk’i, inda kowa ya samu hanya.

Hajiya Turai ce ke ta bala’i, yayin da commissioner Alhaji murtala je zaune yana jinta, ganin bai tankata ba yasa ta nufesa ta bangaje hular dake kansa tana mai cewa “Alhaji da kai nake fa, don wulakanci ka na jina ka barni”.

Wani banzan kallo ya watsa mata yace “nasan dani kike ai, kuma ina jinki, kawai abunda nake so ki sani, duk abunda zaki yi nasan Ramlah muttaqa Gimba sai ta shigo gidan nan, in ma ki kwantar da hankalinki ko akasin haka duk matsalar kice “‘

Hannu tasa a kai ta kwala ihu tare da fad’in ” na shiga uku, yanxu Alhaji dama ‘yar gidan general muttaqa Gimba za ka auro mij, wallahi da sake, ka auri ‘yar kowa amma kada ka auro min ‘yar gidan”.

Kallon raini ya mata yace” oh really, dama kina tunanin irin kuchakar nan zan auro, ai tun dana ga take takenki shi yasa na d’auko miki wacce ko kallon banza kika mata sai kin kwana a guard room, kuma ki sani Ramlah ‘yar gata ce,,sanyin idon gidan general, don haka ki kama kanki ki kama girmanki” ya k’arashw fad’i yana mai fita daga parlourn, zubewa tayi akan kujera tana mai fad’in “na shiga uku, wallahi ba zata sab’u ba, bari in kira Hajiya Atine musan abunyi” ta fad’i tana mai d’auko wayarta.

_*GIDAN GENERAL MUTTAQA GIMBA*_

*_Toh fans, ya kuke ganin za a k’are tsakanin Amaryar Alhaji murtala da Manyan mata?, shin auren zai yiwu kuwa?, shin zasu iya d’aukan matakin?_*

*_Ga kuma maryam, ya zasu k’are da iyayenta da Alhaji?_*

_*Fateeyzah mbs*_ ✍️³¹ ³⁵

MATAR BAHAUSHE? CHAPTER 7 BY Fateeyzah mbs_✍️* - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: The Hon. Margery Christiansen

Last Updated:

Views: 5503

Rating: 5 / 5 (50 voted)

Reviews: 89% of readers found this page helpful

Author information

Name: The Hon. Margery Christiansen

Birthday: 2000-07-07

Address: 5050 Breitenberg Knoll, New Robert, MI 45409

Phone: +2556892639372

Job: Investor Mining Engineer

Hobby: Sketching, Cosplaying, Glassblowing, Genealogy, Crocheting, Archery, Skateboarding

Introduction: My name is The Hon. Margery Christiansen, I am a bright, adorable, precious, inexpensive, gorgeous, comfortable, happy person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.