YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (2024)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU

(_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

Related Articles

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

Bismillahir Rahmanir Rahim.

A hankali wani Yellow Helicopter ya fara saukowa a tsakiyar sunk’umin dajin mai fad’in gaske. yana gama saukowa k’ofar jirgin ta bud’u, ba b’ata lokaci na cikin jirgin suka fara fitowa da sauri-sauri har suka fice ga baki d’ayan su. Mutane biyar ne, Maza biyu Mata uku. Hud’un cikinsu riguna farare ne a jikinsu, sai d’ayar macen dake sanye da red t-shirt, saidai matan sun d’ora wata leather jacket a saman rigunan jikinsu, kansu kuma sanye yake da sun hats, sai wasu black wellingtons boot dake sanye a k’afafuwansu. Ko wanensu akwai k’atuwar Backpack goye a bayan shi.

Dukansu tsaye sukayi suna k’arema dajin kallo wanda yake kallo, don kuwa dajine ba k’arami ba, saidai bayada wadatattun bishiyoyi a cikinshi, saisa duk inda ka d’ora idanuwanka iya ganinka.

“Anya! dajin nan lafiya yake kuwa?”.

Cewar d’aya daga cikin mazan yana cigaba da wulga idanuwansa ta ko ina a cikin dajin. Gefenshi macen mai jan rigan ta iso tana fad’in,

“Wallahi nima dai tambayar da nake yima kaina kenan, ko alamun gari babu a kusa fa”.

“Bamu shigo cikin dajin nan ba saida aka tabbatar min da lafiyarsa”.

Wata matashiyar budurwa fara ta fad’a, tare da kallon wacce ke gefenta tace;

“Hulaim kiyi amfani da na’urar hangen nesa ki dubo muna abunda ke yammancin mu, don kuwa can zamu dosa”.

Kai wacce ta kira da Hulaim d’in ta gyad’a tare da fad’in,

“Okay Ranki shi dad’e!”.

Cikin sauri ta sauko da backpack d’in dake bayanta, ta bud’e tare da ciro wata ‘yar k’aramar Camera. Sannan ta d’anyi nesa dasu tare da saita camerar a yamma ta d’an leka idonta d’aya ta fara hango musu. tsawon wasu mintuna ta juyo tana kallonsu tace;

“Ranki shi dad’e!, akwai gari a gaba, saidai kafin mu isa zamuyi kusan awa d’aya”.

Zaro idanuwa waje mai red t-shirt d’in tayi tana fad’in,

“Awa d’aya fa kika ce?, haba fisabilillahi taya zamu iya tafiyar awa d’aya a cikin wannan daji?”.

D’an murmushi kawai Hulaim tayi ba tare da tace komai ba, ta mayar da hankalinta wurin farar dake fad’in,

“Yanzu k’arfe 7:00am kenan hakan na nufin zuwa 8:30am har mun isa, don haka ya kamata mu hanzarta”.

“Kuzeem! dagaske kuwa dajin nan zamu yanka a k’asa?, ni sai nake ganin abun tamkar a mafalki wallahi”.

Mai red t-shirt d’in ta sake fad’a tana kallon saitin da farar matashiyar budurwar take. ganin tak’i tankata ya sanyata cigaba da fad’in,

“Meyasa jirgin bazai kaimu har cikin garin ba?”.

D’an dafe kai Kuzeem d’in tayi tace;

“Saimah!, inace da yardar ki tare da kuma amincewarki kika biyo mu wurin nan ko?, ba janyoki da k’arfin tsiya mukayi ba”.

A fusace Saimah tace;

“Amma ai ba haka mukayi dake ba, don baki cemin daji zamu yanka haka a k’asa ba tamkar wasu shanu”.

Dariya Su Hulaim sukayi ganin yanda Saimah ke rarraba ido tsoro bayyane a fuskarta. Kuzeem ma taso yin dariyar don tasan dama za’a rina don Saimah itace lamba d’aya a cikin matsorata, saurin gumtse dariyar dake shirin zo mata tayi ta d’ago tana kallon Saimah, fuska a tamke tace;

“Kinga malama idan bazaki je ba, ga can driver a jirgi saiki koma ki zauna kuyi zaman jiran dawowarmu”.

Tana gama fad’in haka tayi gaba, hakan yasa su Hulaim mara mata baya har lokacin suna dariyar Saimah, K’wafa ta saki tana binsu da kallo, kamar zata fasa kuka tabi bayansu, ji take tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida.

Wasa-wasa suka fara nausawa cikin dajin tamkar wad’anda zasu bar duniya, Kuzeem da Hulaim ne a gaba, yayinda Ra’is da Rau’an ke bayansu sai Saimah a bayansu amma sun d’an yimata nisa. D’an gudu tayi ta iso wurin su Kuzeem tana fad’in,

“Haba ku rage sauri ku dena barina a baya manah”.

Babu wanda ya tanka mata suka cigaba da tafiya ba kama hannun yaro, a haka rana ta fara b’ullowa inda dajin yayi haske sosai, tsuntsaye sai shawagi suke a sararin samaniya. Sosai suka sake nausawa cikin dajin. Zuwa wannan lokaci Engeen Oil d’in Saimah ya fara k’arewa don kuwa ba k’arya ta gaji ainun, hannu tasa a gefen bag d’inta ta ciro robar ruwan swan zata kafa baki, cikin azama Kuzeem ta fisge robar ruwan ta cigaba da tafiya tana fad’in,

“Ba zaki sha ruwan nan a yanzu ba, kinfini sanin illar yin hakan”.

Bayanta Saimah tabi da kallo tamkar zata fasa ihu, don wani irin k’ishi take ji kamar zata suma, dak’yar ta iya furta.

“Dan Allah ku tsaya mu huta manah, tunda dai ba gasar zuwa bangon duniya muke yi ba”.

Wannan karon kam har Kuzeem saida ta dara sosai, bayan sun gama dariyar ne suka dakata da tafiyar, don suma d’in suna tattare da tarin gajiya saidai basu son nuna gajiyar ne tun yanzu don kada hakan ya karye musu k’warin gwuiwa.

Ganin sun tsaya ne ya sanya Saimah zubewa zaune a k’asa tana sauke ajiyar zuciya jere da jere. suma zama sukayi kan wasu ‘yan duwatsu dake wurin. Sai a lokacin Kuzeem ta mik’a mata gorar ruwan, cikin sauri takai hannu ta karb’a sannan ta bud’e ta kafa baki, saida tasha sosai kana ta sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya. Baifi hutun mintuna goma sukayi ba, Kuzeem ta mik’e tayi gaba abinta ba tare da tace dasu komai ba. suma su Hulaim mik’ewa sukayi suka mara mata baya, hakan yasa Saimah binsu don ta d’an huta amma sosai k’afafuwanta ke yimata wani irin zugi.

Haka suka cigaba da tafiya Saimah na yimusu mita amma basuda lokacin kulata dole ta hak’ura tayi shiru. zuwa wannan lokaci ko wane daga cikinsu ya gama galabaita sosai, dauriya ce kawai suke yi. ga rana ta fara zafi donma suna sanye da manyan huluna hakan yasa basa jinta sosai, haka suka cigaba da tafiya cike da dauriya, kuma cikin hukuncin Allah basu gamu da kowane irin abun cutarwa akan hanyar tasu ba, hakan ya sanya hankalinsu ya kwanta sosai.

Zuwa wani lokaci sai gasu sun fara cimma gonakin garin, ta tsakiyar wata k’atuwar gona suka ratso, sai a lokacin suka fara maganganu a tsakaninsu, kamar wasa suka fara hango tsirarun gidajen garin da suke tunkara, hakan yasa suka k’ara azama cikin k’ank’anin lokaci suka iso gab da shiga garin mai yalwar bishiyoyin mangwaro ta ko ina.

Basu ankare ba suka fara ganin wasu mutane na dirowa daga saman bishiyoyin mangworon ko wanensu hannunshi rik’e da makami. a k’alla mutanen zasu kai su goma. Cike da mugun kad’uwa sukayi turus! suna kallon mutanen kamar yanda suma kallon nasu suke yi. wai! naso ace kunga idanun mutuniyar mazugal kenan.?

“Su waye ku?, kuma me ya kawo ku a cikin garin mu?”.

Cewar wani dogo d’an shawalwali daga cikin mutanen. Dukansu shiru sukayi suna cigaba da kallon mutanen wad’anda ko daud’ar jikinsu da kayansu kawai abin kallo ce.

“Idan har baku amsa muna tambayoyinmu ba tabbas zamu kashe ku har lahira, mu kuma k’ona gawar ku”.

Cike da matsanancin tsoro, tashin hankali da firgici Saimah tace;

“Kuzeem mu gudu!, zasu kashe mu fa suka ce”.

Hulaim ma da take jaruma amma ganin dagaske fa mutanen nan suke ya sanyata fad’in,

“Ranki shi dad’e!, idan fa muka tsaya mutanen nan zasu iya aikata abunda suka fad’a”.

Kafin Kuzeem ta bata amsa mutanen suka fara tunkaro su gadan-gadan!, ganin haka ya sanya Saimah, Hulaim Rau’an da Ra’is fara yin baya-baya tsoro k’arara a fuskokin su, yayinda Kuzeem tayi tsaye a wurin ko gizau batayi ba, illah cusa hannayenta da tayi a cikin aljihun jacket d’in jikinta tana kallon mutun d’ayan dake daf da k’arisowa inda take a tsaye hannunshi d’auke da wata sharb’eb’iyar adda har wani d’aukar ido take.✍️

Abinda zuciyarta ke raya mata ta aikata tin d’azun shi kawai take sak’awa a ranta, duk da tasan yin hakan abune da zai dasa alamar tambaya a gareta, saidai a halin yanzu batada wata mafitar da ta wuce yin hakan, domin tseratar da rayukansu daga wurin wad’annan mahaukatan mutane. Tana cikin wannan tunanin ne Mutumin ya iso wurinta tare da d’aga addar hannunsa zai sara mata a jiki.

Cikin wani irin salo mai zaman kanshi tayi wata irin d’uk’ewa, hakan yasa ya sari iska kafin yayi yunk’urin juyowa zuwa gareta tayi azamar mik’ewa, cikin zafin nama ta sanya k’afarta d’aya ta kwashe mashi k’afafuwa ta baya, sai gashi a k’asa timm!, ba b’ata lokaci ta ciro d’ayan hannunta dake cikin aljihun jacket d’inta sai ga bindiga ta bayyana, da haka ta saita bindigar a kan Mutumin.

Wani irin zaro ido Ra’is, Hulaim, Rau’an sukayi suna kallon Kuzeem cike da wani irin mugun mamakin yanda ta kai wannan shirgegen mutum a k’asa kamar wani buhun masara, tare da bin bindigar dake hannunta da kallo mai tattare da alamomin tambaya. Ita kuwa dama tasan za’a rina, sai kawai ta basar tare da mayar da dubonta wurin Mutanen da suka nufota saura k’iris su iso inda take, cikin wata kakkausar murya tace;

“Duk wanda ya sake taku d’aya daga cikinku saidai wani ba shi ba”.

Jin hakan ya sanyasu taka wani irin burki ba tare da sun shirya ba, suka shiga kallon yanda ta saita bindigar a kan d’an uwan su, sai rawa jikinshi ke yi tsabar tsoro da firgici.

“Ku ajiye makamanku a k’asa”.

Ta sake fad’a cike da bada umurni, ba b’ata lokaci duk suka aje makaman jikinsu sai rawa yake. fuskarta bayyane da tsantsar b’acin rai tace;

“Meyasa kuke d’abi’u irin na mahaukata?, shin kunsan mu su waye da kuke k’ok’arin kashe mu?”.

Su dukansu cikin sauri suka shiga girgiza mata kai alamar a’a. D’an cije lips d’inta na k’asa tayi kana ta juya ta watsawa abokan tafiyar nata wani mugun kallo, hakan yasa suka iso wurin ko wannensu na rarraba ido, cike da jarumta tare da rashin nuna tsoro ta iso gaban mutanen tana cigaba da fad’in,

“Mu ma’aikatan lafiya ne da gomnati ta turo mu garin ku domin duba lafiyar ku, amma abun mamaki sai gashi ku kuna k’ok’arin rabamu da rayuwar mu, shin miye ribarku idan kun aikata hakan?”.

Nan wasu daga cikinsu suka fara magana.

“Don girman Allah kuyi muna aikin gafara likita, wallahi rashin sani ne ya sanya muka aikata muku haka, muna baku hak’uri”.

Bayan sunyi shiru ne wani d’an matashin saurayi mai jini a jika, wanda shigarsa ta d’an bambanta da mutanen ya fara magana cikin nutsuwa.

“Likita abunda yasa kuka ga mun aikata muku haka domin kare rayukanmu ne, saboda duk cikin kwanakin nan bamuda natsuwa tare da kwanciyar hankali, domin kuwa kullum cikin farautar rayukan mu akeyi, hakan yasa muka shirya daukar mataki tun kafin akai ga samun cin galaba a kanmu “.

Kai ta girgiza alamar gamsuwa sannan tace;

“Kenan hakan na nufin akwai wasu b’ata garin dake son shigo muku cikin gari domin musgunawa rayuwarku?”.

“Eh hakane, s…”.

Hannun da ta d’aga mishi ne ya sanyashi dakatawa daga maganar da yake yi.

“Da yardar Allah komai zaizo k’arshe, yanzu muna buk’atar kuyi muna jagora a cikin garin naku domin mu tabbatar da lafiyarku, sannan kuma zamu d’an zazzagaya ta bayan garin saboda mu tantance idan babu wasu k’wayoyin cuta a cikin garin naku”.

Nan take fuskokinsu suka bayyana jin dad’in hakan tare da nuna gamsuwarsu, suma su Hulaim sosai suka jinjinama jarumtar Kuzeem tare da k’arfin halinta. Daga haka Mutanen sukayi musu jagora zuwa cikin garin nasu, duk inda suka gilma sai an bisu da kallo cike da k’auyanci. Kai tsaye fadar Hakimin garin dake tsakiyar gari Mutanen suka kaisu, inda jama’ar garin suka lullub’esu suna kallo. Nan wasu daga cikin Mutanen sukayi ma Hakimin bayani kamar yanda Kuzeem tayi musu. cike da nuna jin dad’inshi yayi lale marhaban dasu tare da yi musu ban gajiya, Wannan lokacin Rau’an ne yace;

“Mun gode sosai, to alhmdlh a halin yanzu dai mun gama tabbatar da lafiyar ku, sai abunda ya rage muna shine mu d’an zagaya ta bayan garin”.

Hakimin na murmusawa yace;

“To ba shan kai!, ai ga matasan garin nan sai suyi muku ja gaba ko?”.

Hulaim ce tayi saurin fad’in,

“A’ah ba buk’atar hakan, domin kuwa da akwai feshin maganin da zamuyi wanda idan har wani wanda ba mu ba ya shak’esa tabbas zai iya cutar dashi, bayan haka muna so ga baki d’aya a natsar da kowa a garin nan manya da yara saboda kar su isa inda zamuyi feshin maganin”.

Cike da gamsuwa yace;

“Ba matsala, zaku iya tafiya yanzu, na baku damar ku shiga duk inda kuke so a cikin garin nan”.

Da wani irin kallo Kuzeem ta bishi tare da sakin wani guntun murmushi wanda ita d’ai tasan ma’anarshi, sai kuma a hankali cikin wani irin salo ta d’an juya idanuwanta saitin saurayin da sukayi magana da ita a wajen garin, tayi masa wani irin signal da ido ba tare da kowa ya lura da hakan ba, daga haka ya fakaici idanuwan mutane ya sulale daga wurin.

Sake kallon Hakimin tayi sannan tace;

“Muna godiya sosai”.

Tana fad’in haka ta mik’e suka bar wurin, nan suka fara zaga cikin garin har suka iso bayan garin mai cike da wasu irin gingima-gingiman duwatsu masu girman gaske. Zuwa wannan lokaci kowane daga cikinsu yunwa ta fara azalzalar sa hakan yasa tuni bakin Saimah ya mutu saidai kallo d’aya zakayi mata ka hango tarin gajiya, galabaita, yinwa tare da mashahurin tsoro a cikin k’wayar idanuwanta domin kuwa har yanzu ta kasa cire tsoron abinda ya faru, kan wasu k’ananun duwatsu suka zauna, suka d’an tab’a drinks da snacks d’in da sukayo guzuri, sai a lokacin suka d’an fara jin normal, amma fa suna tattare da tarin gajiya.

“Wallahi duk abinda ya faru muna komawa gida zan kira Ammah in sanar da ita, ke shikenan ko kad’an baki damu da rayuwarki ba?, da ace Allah baisa akwai bindigar a hannunki ba shikenan kin tsaya sun halaka ki”.

Cewar Saimah tana bin Kuzeem da wani mugun kallon takaici. d’an murmushi Kuzeem tayi sannan tace;

“Dr! Ina so ki fahimci cewa sai an cire tsoro ake haifar da tsaro!!!. Tun tashina na gane sabo da wahalar rayuwa, gwagwarmaya tare da juriya sune matakin cin ko wace irin nasara a rayuwa, idan har tsoro zai rufe zukatanmu taya kike ganin zamu kai ga cin nasara”.

“To amma ai ba’ace ka jefa rayuwarka a cikin had’ari ba ko?, Ina ce su abokanan aikin naki guduwa sukayi da suka ga bala’i na tunkaro su, amma ke dayake zuciyar dutse gareki sai kika tsaya”.

Had’e rai Kuzeem tayi tace;

“Ke kika damu da rayuwa, nikuwa rayuwata da lafiyata duka na sadaukar dasu wa k’asata har sai burina ya cika wurin ganin na dawo da martabar k’asata”.

Raf! Raf!!

Su Hulaim suka shiga tab’a mata suna murmushi, Saimah kuwa harara ta shiga watsa musu tare da jan guntun tsaki, ita dai Kuzeem bata sake cewa komai ba daga haka ta mike tana fad’in,

“Ina zuwa”.

Bata jira jin wani abu daga garesu ba tayi gaba, su kuwa da kallo kawai suka bita. Saida tayi tafiya mai d’an tsayi sannan ta iso wurin saurayin, bayan wani dutse suka dawo gudun kar wani ya hango su.

“Bilal har yanzu dai babu wata matsala ko?”.

Kai ya girgiza mata yace;

“Eh babu”.

Daga haka yasa hannu a aljihun wandonsa ya ciro wani flash drive yace;

“Dukkan hujjojin da muke buk’ata suna a ciki tare da wasu muhimman bayanai”.

“Okay, hoton yarinyar fa?”.

“Har shi yana ciki, sannan a halin yanzu tana k’asar UK, akwai buk’atar ki sameta a can aikin mu zaifi tafiya yanda muke so”.

“To amma Bilal taya kake ganin hakan zai yiwu?”.

“Abune mai sauk’i Kuzeem!, zamuyi waya idan kun isa, amma miye hikimarki ta zuwa da wad’annan ‘yan jaridar a nan?”.

“Karka damu da wannan, saidai fa akwai wata ‘yar matsala bindigar da suka gani a hannuna”.

“Inada tabbacin kinsan hanyar da zakibi wurin kare kanki, ya kamata ku kama jiki kubar garin nan saboda tsaro, nima zuwa jibi zan b’ace b’at!”.

D’an jujjuya flash drive d’in ta shiga yi tana k’are masa kallo sannan tace;

“Bilal kai jarumi ne, hak’ik’a na jinjinawa jarumtar ka”.

“A’ah duk wata jarumta tana biyowa bayan taki jarumtar Kuzeem”.

D’an guntun murmushi ta saki tace;

“Ka kula sosai, na barka lafiya”.

Kai kawai ya gyad’a mata baice komai ba, daga haka ta juya ta bar wurin sannan shima ya wuce.

A can cikin garin kuwa su Kuzeem na barin wurin Hakimin yayi saurin mik’ewa ya koma cikin gidan shi, bai zarce ko ina ba sai d’akinshi, rawanin shi ya cire don wani zufa ne ya shiga karyo mishi, danne-dannen yar k’aramar wayar nokia dake hannunshi yayi sannan ya kara wayar a kunnenshi, yana jin alamar an d’aga kiran yace;

“Mai gida wallahi akwai matsala fa, don kuwa yanzu haka wasu mutane sun shigo garin nan wai gomnati ta turosu domin duba lafiyar mu”.

“What!!!?”.✍️

✍️*Anup*?⁶ ¹⁰

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Nathanial Hackett

Last Updated:

Views: 5507

Rating: 4.1 / 5 (52 voted)

Reviews: 91% of readers found this page helpful

Author information

Name: Nathanial Hackett

Birthday: 1997-10-09

Address: Apt. 935 264 Abshire Canyon, South Nerissachester, NM 01800

Phone: +9752624861224

Job: Forward Technology Assistant

Hobby: Listening to music, Shopping, Vacation, Baton twirling, Flower arranging, Blacksmithing, Do it yourself

Introduction: My name is Nathanial Hackett, I am a lovely, curious, smiling, lively, thoughtful, courageous, lively person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.