YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (2024)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU

(_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (1)

Www.bankinhausanovels.com.ng

Related Articles

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

  • YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

“Good morning everyone!. I’m L.G(Lieutenant General) Aliyu Iko”.

*_Raf! Raf!! Raf!!!_*

Suka shiga tab’a mishi cike da girmamawa, hakan ya bani tabbacin shi d’in babba ne sama da su. D’an murmushi yayi sannan ya cigaba da fad’in,

“Ah! da farko dai ina yimuku barka da isowa wannan muhimmin meeting, ina fatan dukkanku kun iso lafiya?”.

A tare suka girgiza mishi kai alamar eh. Fita yayi daga masaukinshi, ya nufi wurin wata k’atuwar Computer dake ajiye cikin hall d’in daf da inda suke tana fuskantar su, hakan yasa duk suka maida hankalinsu a kan Computer da zanen wani k’aton map ya bayyana a cikinta.

“Kamar yanda kuka sani wannan TASWIRAR k’asar SARBIK ce. A k’alla munada jahohi 40 a cikin wannan k’asa mai tarin albarka. Kowa ya san shekarun da suka gabata k’asar SARBIK ta kasance k’asa mai dawwamammen zaman lafiya, cigaba tare da wadatar arziki da albarkatun k’asa. Kafin yanzu ta zama hedikwatar tashin hankali da rashin zaman lafiya. Musamman a wad’annan jahohin RISAM, RADDAL, GAITO, SABALI, MANUN, TALBI abun yafi tsamari a cikinsu. Inda cikin k’ank’anin lokaci munyi asarar rasa rayukan biliyoyin mutane wad’anda ‘Yan ta’adda ko ince ‘yan tada k’ayar zaune suka kashe basuji ba basu gani ba. Wanda gomnatin k’asar nan a koda yaushe tana cikin yin iya k’ok’arinta wurin ganin zaman lafiya ya wanzu a cikin wannan k’asa amma abun ya citura, saima k’ara hudowa wasu sabbin matsalolin sukeyi ta hanyoyi daban-daban”.

D’an shiru yayi tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya maida dubonshi saitin Kuzeem, yace;

“Kuzeem Yusuf Garba! ko zaki iya fad’a muna meyasa abun yak’i ci yak’i cinyewa?, har zuwa wannan lokaci. Ina nufin a ina matsalar take?”.

Kafin Kuzeem d’in tayi k’ok’arin furta wata kalma. Wani saurayi da zai kai 34 years yayi saurin mik’ewa rai b’ace, tare da k’amewa yace;

“Sir! a ganina manya ya dace ka fara ba dama su tofa albarkacin bakinsu, kafin ka ba wannan yarinyar mai k’aramin matsayi a cikin mu”.

Cikin sauri wasu daga mahalarta meeting d’in suka shiga girgiza kai alamar bashi goyon baya akan abinda ya fad’a.

“Major Khalil! shin hakan da ka fad’a yana nufin ka fini sanin abinda ya dace inyi?, ko kuwa kana son koyamin yanda zan gudanar da aikina ne huh?”.

L.G Aliyu Iko ya tambayeshi yana kafeshi da idanuwanshi, bai ko kalli masu bashi goyon bayan ba. Kai yayi saurin girgiza mishi sannan yace;

“No Sir! ba hakan nake nufi ba…”.

Saurin d’aga mishi hannu L.G Aliyu yayi, fuskarshi ba yabo ba fallasa yace;

“Ya kamata ka duba kalamanka nan gaba”.

“I’m sorry Sir!”.

Major Khalil d’in ya sake fad’a masa, sannan ya zauna yana mai jin haushi a ranshi. Kuzeem kuwa ko inda inuwar Major Khalil d’in take bata kalla ba, tayi saurin mik’ewa tare da k’amewa tana kallon L.G sannan tace;

“Yes Sir!!!”.

“Muna saurarenki”.

Ya fad’a mata yana dawowa ya zauna. Abun sautin maganar da ke gabanta ta gyara, kana ta fara magana cike da kamala.

“Sir! Nidai a iya hasashena, saboda akwai b’ara gurbi a cikin manyan k’asar nan, wad’anda suke yimuna zagon k’asa tare da yankan baya ta hanyoyin da bamuyi zato da tsammani ba. Hakan yasa ko an k’irk’iro hanyoyin da za’ayi amfani da su wurin ganin an magance matsalolin dake addabar wannan k’asa sune ke shiga da fita har sai sunga sun b’ata shirin, wannan dalilin ne yasa har yanzu matsalar kasar nan ta kasa kawowa k’arshe”.

_*Raf! Raf!! Raf!!! Raf!!!!*_

Meeting hall d’in ya kaure da tab’i ta ko’ina, dukansu sai girgiza kai suke cike da gamsuwa da abinda Kuzeem ta fad’a, banda Khalil da ya tsuke face kamar wanda aka aikowa da sak’on mutuwa. Murmushi L.G Aliyu yayi cike da alfahri da ita, sannan ya nuna mata mazauninta alamar ta zauna, daga haka Kuzeem ta zauna, tana gyara zaman veil d’in kanta.

“Kaifa Major Khalil ko kanada abun cewa?”.

L.G Aliyu ya fad’a yana maida dubonshi saitin Khalil d’in. Fuska a murtuk’e ya mik’e tare da k’amewa sannan yace;

“No Sir!..”.

Yana gama fad’in haka ya koma ya zauna tare da furzar da wata iska daga bakinshi cike da jin haushin Kuzeem, yana ta sak’a abubuwa da dama a ranshi har aka kammala meeting d’in bai sani ba, saida wanda ke gefenshi ya d’an tab’oshi sannan ya d’ago, nan yaga duk an watse. Cike da mugun takaici ya mik’e ya fice daga hall d’in.

*2 days later*

Tsaye suke a gaban wani kangon gida, dukansu sanye suke da wata monkey jacket bak’a dake d’auke da harafin *S* a tsakiyarta wanda aka sak’ashi da farin zare. Wata budurwa na k’ok’arin kutsa kanta cikin k’ofar shiga gidan, Kuzeem tayi saurin rik’o hannunta tare da maidota baya da k’arfi. Saurin kallonta budurwar tayi, tace;

“Yadai?, Kuzeem!”.

“Meerah! ba ta wannan hanyar ya dace mu shiga ba”.

Inji Kuzeem ta bata amsa. Girgiza kai wani matashin saurayi dake gefensu yayi yace;

“Eh haka ne, ta window ya kamata mu dira, sai wasu daga cikinmu su tare bakin wannan k’ofar.”.

Cikin sauri wasu mutum biyu suka iso bakin k’ofar, yayinda sauran suka zagaye kangon gidan, su Kuzeem kuma suka nufi bayan gidan, daidai wata k’atuwar window suka tsaya, a hankali saurayin ya d’an lek’a kanshi ciki.

“Mu shiga”.

Ya fad’awa su Kuzeem sannan ya dira cikin d’akin, da sauri suma suka dira tare da nufar k’ofar fita d’akin sai gasu sun b’ullo ta cikin wani d’aki, amma har lokacin basu ji motsin kowa ba, hakan yasa suka cigaba da shige da fice a cikin d’akunan da ke kangon gidan saboda sunada tabbacin akwai mutane a cikin gidan. Dariyar da suka jiyo ne daga cikin wani d’aki ya sanyasu saurin k’arasawa wurin d’akin, cikin sand’a suka fara kutsa kawunansu a ciki.

A tsakiyar d’akin suka hango wasu gungun matasa sunata busar hayak’i, yayinda wasu ke buga k’arta. Cikin sauri suka k’araso wurinsu tare da saita bindigogin da ke hannunwansu a kan mutanen, a mugun rud’e mutanen suka d’ago suna kallonsu cike da tsoro da tashin hankali.

“Ku mik’a wuya, kuma zan harbi duk wanda yayi yunk’urin guduwa daga cikinku”.

Kuzeem ta fad’a musu tana gyara rik’on bindigar hannunta. Jikinsu na rawa sukayi kneeling tare da d’aga hannayensu sama. Wani daga cikinsu ne ya shammace su ya ruga da gudu ya dire ta window ya fad’a cikin wani d’aki, da gudu Kuzeem tabi bayanshi itama ta dire ta windown yana k’ok’arin ficewa daga d’akin tayi azamar d’auke k’afarshi ta hagu da bindiga, hakan ya sanyashi sakin wata irin k’arar azaba tare da zubewa wurin a sume. Daga haka ta kira sauran abokanan aikinta dake can waje a waya, cikin sauri suka iso d’akin, nan suka tasa k’eyar mutanen a gaba zuwa waje, yayinda wasu daga cikinsu suka tallabi wanda Kuzeem d’in ta harba, sannan suka fice daga kangon gidan.

Bayan Hilux d’insu suka tura mutanen yayinda wasu suka zauna tare da su a bayan. Su Kuzeem kuwa wata k’aramar mota suka shiga, sannan suka bar wurin cike da jin dad’in nasarar damk’e wad’annan mutane da suka d’au tsawon lokaci suna hak’ak’e, amma sai yau Allah ya basu galaba a kansu. Ba kamar Kuzeem da operation d’in yake a k’ark’ashin kulawarta, duk ta fisu farin ciki.

Kuzeem na zaune office d’inta tana shigar da wasu bayanai akan mutanen da suka kamo. Major Khalil ya shigo cikin office d’in tamkar an jefosa daga sama don ko sallama baiyi ba, a bakin k’ofa ya ja ya tsaya, fuskarnan tashi a murtuk’e kamar bai tab’a dariya ba yace;

“Keee! wa ya baki izinin yin harbi?”.

D’an d’agowa tayi ta kalleshi sannan ta mayar da hankalinta akan abinda take yi, don karma ya b’ata mata lokaci. Hakan da tayi ba k’aramin sake tunzurashi yayi ba, a mugun fusace ya iso gabanta tare da sa hannu ya rufe laptop d’in da take amfani da ita yana fad’in,

“Harke wacece?, da ina tambayarki zakiyi kunnen uwar shegu da ni, me kike jin kanki ne?”.

Tuni zuciyarta ta kawo har wuya, amma fahimtar abinda yake son gani kenan wato b’acin ran nata, ya sanyata dakewa tare da shanye b’acin ran. Wannan ba shine karon farko da Major Khalil ke k’alubalantarta akan aikinta ba. Ta rasa sanin mai ta tare mishi a hukumar?, da ya d’ora mata karan tsana, hakan yasa duk abinda yake yimata bata kulashi, ba wai don tana tsoronshi ba, sai don shi d’in yana sama da ita, kuma ta san artabunsu bazai yi kyau ba. Amma yau ya kaita mak’ura dole ta ja mishi kunne a karo na farko.

“Sir Khalil ka fita sabgata, kayi abinda ke gabanka”.

Kuzeem ta fad’a mishi tana kallon tsakiyar idanuwanshi don son danne b’acin ran da take ciki. Ba k’aramin kwarjini idanuwanta sukayi mishi ba hakan yasa yayi saurin janye idanuwanshi daga cikin nata, sannan ya saki wani shu’umin murmushin jin dad’in kulashin da tayi a karo na farko, saboda rashin kulashin da batayi yana daga cikin abubuwan dake k’ara haddasa k’iyayyarta a cikin zuciyarshi.

“Idan har kikaga na fita sabgarki to kuwa kin daina kai kanki matsayin da Allah bai kaiki ba, kuma dole ne ki amsamin tambayata a yanzu, waye ya baki izinin yin harbi?”.

“Idan nak’i fa?”.

Ta fad’a kai tsaye ba tare da fargabar komai ba. Kujerar dake ajiye wurin yaja ya zauna tare da d’ora k’afarshi d’aya kan d’aya yace;

“Zaki fuskanci mummunan hukunci ta hanyar da bakiyi tinani ba…”.

Tun kafin ya k’arasa fad’in maganar tayi saurin mik’ewa tsaye tare da d’aukar bindigar dake ajiye gabanta, tayi saiti da kanshi tace;

“Kaima ina so ka gwada aikata makamancin laifin da ya dace a hukuntaka kaga idan ban harbeka ba”.

_________Da wani irin mugun shock Major Khalil ke kallonta don bai tab’a tsammanin zata iya yimishi haka ba, saboda ba yau ya saba k’alubalantarta ba amma bata tab’a yunk’urin yimasa wannan barazanar ba. Wani ja’irin murmushi Kuzeem tayi ganin tsoro k’arara a k’wayar idanuwanshi, a hankali ta janye bindigar sannan ta nuna mishi hanyar fita tace;

“Excuse me!”.

Cikin sauri ya mik’e yana yimata wani kallo mai tarin ma’anoni, ga kuma wani k’ululun bak’in cikin dake taso mishi a zuciya a kan wannan wulak’ancin da tayi mishi, Allah yasa ma ba’a gaban kowa ba ne da yau ta gama da shi yanda yake d’aukar kansa wani shege ace wannan yarinyar tayi mashi barazana da bindiga a gaban idon mutanen da suke bashi girma.

“Mu zuba mu gani!”.

Ya fad’a mata cikin wata irin murya mai wuyar tantancewa, daga haka ya fice daga office d’in kamar zai tashi sama. Saurin ja da baya Meerah dake k’ok’arin shigowa office d’in tayi tana bin bayanshi da kallo, sannan ta girgiza kai ta shiga, ganin Kuzeem tsaye ya sanyata saurin isowa wurinta tace;

“Kuzeem lafiya kuwa?. Me Sir Khalil yazo yi a office d’inki?”.

D’an dafe kai Kuzeem tayi sannan ta koma ta zauna, tare da lumshe idanuwanta na ‘yan wasu sakanni sannan ta bud’e idanuwan ta kalli Meerah tace;

“Har sai yaushe zai daina takurawa rayuwata ne?”.

“Kiyi hak’uri Kuzeem, hassada ce kawai ke addabarshi, dama shi haka yake da zaran yaga kana cigaba tofa zai d’orama karan tsana, duk wata hanya da zaibi wurin ganin ya b’ata ma rai sai yayi amfani da ita”.

“To kuwa a kaina hassadar tashi zata kawo k’arshe, bazan zauna in zuba ido k’aton banza yana takani son ranshi ba, wallahi babu ruwana da matsayinshi yafi nawa, duk yanda yake so haka zamuyi, da ni yake zancen!”.

Kuzeem ta fad’a a zafafe tana sake maida idanuwanta ta lumshe don tuni suka sanja launi daga fari zuwa ja tsabar k’unar rai.

“Abinda yake so kenan yaga kin biye mishi kuna artabu a tsakaninku, shi baiyi gaba ba kema ya hanaki yin gaba. Idan kika zauna kikayi tinani wannan ma wani matakin nasara ne da rayuwarki ta fara takawa Kuzeem, duk wanda kikaga ba’a yima hassada a rayuwarnan to shid’in ba kowa ba ne. Ni nasan da ace Sir Khalil bai hango nasarori a tare dake ba wallahi bazai tsaya yana bibiyar lamurrankin ba. Shawarar da zan baki kiyi watsi da sha’aninshi a gefe, ki fuskanci muhimman abubuwan dake gabanki”.

Meerah ta fad’awa Kuzeem tana dafa shoulder d’inta, don ta lura Kuzeem d’in ba k’aramin b’aci ranta yayi ba. A hankali ta bud’e lumsassun idanuwanta a kan Meerah, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace;

“Shikenan Meerah, nagode”.

Murmushi Meerah tayi mata sannan ta d’auki wasu files dake kan table ta bar office d’in, yayinda Kuzeem ta cigaba da aikin da take yi, b’angare d’aya na zuciyarta tana maimaita *HASBIYALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL* Sannu a hankali ta fara jin b’acin ran da take ciki yana gushewa.

Zaune suke a dining suna dinner, daidai lokacin wayar Kuzeem ta fara ruri alamar shigowar kira. Fuskarta d’auke da wani k’ayataccen murmushi tayi saurin d’aga kiran tare da sa handsfree tace;

“Abbanah!”.

Daga can b’angaren yace;

“Na’am ‘Yar Lelenah ya aiki?, ina fatan babu wata matsala dai ko?”.

“Alhamdulillah Abba”.

Ta fad’a mishi har lokacin murmushin fuskarta bai gushe ba. sun d’au tsawon wani lokaci suna waya da Abban, kai da ganin yanda suke wayar kasan akwai shak’uwa da k’auna a tsakanin Uba da ‘yar tasa. Sai daga baya ta mik’awa su Raudah suma suka gaisa da shi sannan Ammah ta karb’a tare da mik’ewa ta koma d’akinta.

*_Wace ce Kuzeem?_*

Alhaji Yusuf Garba shine cikakken sunan mahaifinta. D’an asalin jahar RADDAL ne, amma a yanzu yana zaune ne da iyalansa a *F.C.T FUNADE* (Babban birnin k’asar SARBIK). Alhaji Yusuf mutum ne mai mugun son abin duniya, tare da dogon buri, wanda hakan ya sanyashi kutsa kanshi a wuraren manyan mutane da kuma manyan ‘yan siyasa, har saida ya samu shima ya zama wani abu a cikin k’asar SARBIK, mutum ne shi mai tsattsauran ra’ayin rik’au, ya san darajar nairah fiye da tunanin mai karatu. Matarsa d’aya Hajiya Hafsa(Ammah) kyakkyawar bafulatana mai kyawon hali, ga ilimi tare da rik’o da addini, ita ‘yar jahar GURD’O ce. Ammah tana fama da ciwon Asthma wanda tun tana yarinya take fama da shi, anyi magani amma babu sauk’i, don likitoci sunsha shaida mata cewa ta gado ce da wuya ta rabu da ita. Ba k’aramar wahala take sha ba duk lokacin da ciwon ya taso mata wanda ke mugun susuta ahalin nata.

Yaransu Biyar duk mata. Maryam, Zulaihat, Fatima(Kuzeem), Raudah sai Rukayya(Deedee). Maryam da Zulaihat tuni sukayi aure harma sun haifafa, inda Maryam ke auren wani hamshak’in mai kud’i kuma d’an siyasa wanda yayi suna a cikin k’asar SARBIK. Zulaihat kuwa wani babban d’an kasuwa ne take aure. Wannan tsari ne na Alhaji Yusuf na aurar da yaransa ga shahararrun masu kud’i wad’anda suka amsa sunansu, don a cewarsa tunda yaransa kyawawane na gaban kwatance bazasu tab’a auren talaka ba, ko masu k’aramin arziki. (Readers kuji fa??) Mutane da dama suna k’aunar su amma babu fuskar tunkararsu, don kuwa koda ace kanada kud’in indai bakayi suna sosai ba bazai tab’a baka damar ganawa da ‘ya’yansa ba, wannan dalilin ne yasa mutane suka sha jinin jikinsu.

Tun Kuzeem na yarinya ta taso da rashin tsoro na ban mamaki, don kuwa duk wani abu da zakai mata bazai tab’a tsorata ta ba, hakan yasa Abba kaita wata babbar asibiti don a duba masa ita ko lafiya take?, saboda akwai wani lokaci sanda suna zaune a RADDAL b’arayi suka shigo gidansu ga lokacin Abba yayi tafiya, nan kowa na gidan ya b’uya don ceton ransa amma banda Kuzeem da tayi zaunenta a palor, tana kallon b’arayin suma suna kallonta, gata a lokacin ‘yar mitsitsiya da ita, duka bata wuci shekara biyar ba, gata da shegen kyau ga gashi tubarkallah, wannan ne ya tsorata b’arayin suka arce don sunyi zaton gamo sukayi da d’iyar aljanu. Shine da Abba ya dawo ana bashi labari ya sungumeta suka je asibiti don a duba mishi lafiyarta, nan aka tabbatar masa da k’alau take kawai halittarta ce haka. Har zuwa yanzu da ta girma bata san menene tsoro ba sam, sannan tanada zafi sosai kamar wuta saidai wani lokacin tafi wuta sanyi.

A duniya Kuzeem bata da wani buri a rayuwarta da ya wuce son yin aikin jarida, hakan yasa bayan ta kammala Secondary school d’inta a *COMMAND INTERNATIONAL SCHOOL RADDAL* ta wuce k’asar Australia tayo Mass comms degree. Saidai kunsan komai nufin Allah ne, sai Allah bai nufeta da aikin jaridar ba, don kuwa tun lokacin da ta dawo ta fuskanci halin da k’asarta SARBIK ke ciki na rashin zaman lafiya da rashin tsaro ya sanyata sanja ra’ayinta. Nan ta sanarma Abba tana so taje aikin Soldier saboda itama ta taka muhimmiyar rawarta wurin ganin ta bayar da gudunmawar tsaro a cikin k’asarta, amma Abba yace sam bai aminta ba, saboda tsananin k’aunar da yake yimata bazai so wani abu ya sameta ba. Daga baya ne tace dan Allah ya barta taje training *DSS* Amma fafur Abba yak’i amincewa, har Ammah bata bada goyon baya ba, sai da sukaga Kuzeem ta shiga damuwa sosai, don ko abinci k’aurace masa tayi, hakan yasa suka amince tare da yimata addu’ar samun nasara. Ba k’aramin farin ciki tayi da amincewarsu ba. Inda saida suka shafe 8 months suna training kana aka tantancesu aka d’aukesu aiki a babbar hukumar *DSS* dake cikin FUNADE wacce duk fad’in k’asar SARBIK babu irinta, saboda hukuma ce da ta zauna da k’afafunta, yayinda gomnatin k’asar SARBIK ke mugun ji da hukumar. K’wazon Kuzeem da jajircewarta a kan aikinta tare da rashin tsoronta wanda ko wani namiji albarka ya sanya aka bata babban matsayi a hukumar, wanda a halin yanzu tana cikin manya-manyan jami’an da hukumar ke ji da su take kuma alfahri da samun su, saboda cigaban da suke samarwa a cikin hukumar wanda sanadin hakan darajar hukumar tasu ke k’ara hauhawa a koda yaushe.

Kuzeem tanada masoya ba kad’an ba, saboda tafi sauran ‘yan uwanta kyau, idan aka ce kyau ba wai hasken fata ba, don sau tari wasu fararen fatar idan kayi musu kallon tsaf zaka gane ba wani kyau ne da su ba, hasken ne kawai. Kuzeem kuwa akwai hasken kuma akwai kyaun, don tun a kallon fari zaka tabbatar da tsantsar tarin baiwar kyaun da Allah yayi mata, bansan yanda zan misilta muku kyaun Kuzeem ba, kawai ku k’iyasta da kanku. Wannan dalilin ne ya sanya Abba ya d’ora dogon buri a kanta, duk da kuwa ya san halin mutuniyar tasa, ita kuwa dama aikinta shine kawai a gabanta bata ma kawo zancen soyayya nan kusa ba ballantana aure. Ammah tayi fad’a har ta gaji ta zuba mata ido, don kuwa wani lokacin Abba ne ke goya ma Kuzeem d’in baya akan ba yanzu zatayi aure ba.

Wannan kenan.

************

Around 10:00am Suka shiga meeting d’in gaugawa a general meeting hall d’insu da ke k’asa, sanadiyar tserewar/guduwar mutum d’aya daga cikin mutanen da suka damk’o. Inda meeting d’in ya haifarwa mutane da dama matsanancin b’acin rai, cikinsu kuwa harda Kuzeem, don tana cikin manyan jami’an da aka d’orawa laifin sakacinsu ne ya sanya mutumin ya gudu, Ita kam rasa ma abunda zata ce tayi, dak’yar dai aka samu aka shawo kan matsalar tare da nemo hanyoyin da suka dace abi wurin ganin an damk’o mutumin cikin k’ank’anin lokaci, sai 11:30am aka kammala meeting d’in. Yayinda Kuzeem tayi zaune a wurin tana ta binciken miye laifinta a cikin wannan lamarin?. K’amshin turaren Major Khalil da taji ya ziyarci hancinta ne ya tabbatar mata da isowarshi a wurin. Da wani irin kallo ya shiga bin ta, kana ya k’yalk’yale da wata dariya. Hakan yasa tayi saurin mik’ewa tana mishi wani irin kallo da idanuwanta da suka sanja launi tsabar b’acin ran da take ciki wanda baya misiltuwa.

“Ya da wannan kallo haka?, kodai kinaso ki huce haushin da kike ciki ne a kaina?, to bani na kar zomon ba rataya aka bani”.

Major Khalil ya fad’a mata yana sakin wani murmushi cikin yanayin farin ciki da annushuwar kallon b’acin ran da ke bayyane a kan fuskarta. Sosai ranta ya koma b’aci ganin iskancin da yake yimata duk da dai ba wannan ne karo na farko ba saidai na yau d’in yafi k’ona mata rai. Cikin sauri Meerah ta jata suka fice daga hall d’in.

*After 2 days*

“Zaka fad’a muna yanda akayi ka gudu?, ko kuwa saina fasa k’wak’walwar kanka da alburushi, na jefawa karnuka gawarka sunyi kaca-kaca da ita”.

Kuzeem ta fad’a a mugun fusace tana kallon mutumin dake durk’ushe a gabanta cikin wani babban d’aki. Cikin rawar murya mai cike da tarin wahala yace;

“Wallahi zan fad’a”.

“Muna saurarenka”.

Inji saurayin dake tsaye gefen Kuzeem hannunshi rik’e da kulkin da ya gama jibgar mutumin.

“Tsakiyar dare ina zaune sauro ya hanani bacci, sai naga an bud’e k’ofar d’akin da muke ciki, wani mutum ya shigo da bak’ak’en kaya hatta fuskarshi a rufe take da bak’in k’yalle, sai ya haskani yaga banyi bacci ba kuma a lokacin duk sauran abokaina sun dad’e da yin bacci. Sai yace min inaso ya taimakeni in gudu?, nace masa eh, to shine fa yace in biyoshi kunji silar guduwata wallahi”.

Kallon juna sukayi cike da mamaki, sannan Kuzeem ta girgiza kai tana sakin wani guntun murmushi, don tuni zuciyarta ta hasko mata bakin zaren. Daga haka aka maidashi cikin ‘yan uwanshi tare da k’ara musu tsaro na musamman. Su Kuzeem kuwa cikin wani k’aton room suka shigo, zama tayi gaban wata Computer, sannan tace;

“Bilal! ina zargin Sir Khalil ne zai aikata hakan”.

“Amma meyasa kike wannan zargin?”.

Bilal ya tambaya cike da mamaki. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, sannan tace;

“Shi kad’ai na san zai iya aikata hakan don cikar wani buri nashi a kaina. Kasan dai yanda yake zazzafar adawa da ni, to zai iya yin komai don ganin ya bak’antamin tare da b’ata ni a cikin wannan hukuma. Kuma a ranar da akayi meeting ina ankare da yanayin da yake ciki na farin ciki. Saidai ni a lokacin zuciyata bata hasasomin komai ba sai a yau”.

Kai Bilal ya girgiza yace;

“Tabbas hasashenki yana bisa gab’a Kuzeem, to yanzu wane irin mataki kikaga ya dace mu d’auka a kanshi?, don gudun abunda kan iya faruwa nan gaba”.

“Ba buk’atar d’aukar wani mataki Bilal, don kuwa bazai k’ara samun wata dama makamanciyar haka ba. Kana ganin yanda yasha jinin jikinshi tun lokacin da muka kamo mutumin nan, nasan yanzu haka yana can cikin tarin fargaba da tsoro, saboda yasan wannan mutumin idan yaji azabar da bazai iya jura ba dole ya fad’i gaskiya”.

“Hakane kam, ya kamata muyi hanzarin shigar da wannan bayanin”.

“Eh zamuyi hakan saidai Sir Khalil d’in ne bazai shigo ciki ba”.

“Meyasa?”.

“Saboda bamuda wata k’wak’k’warar hujja a kansa tunda mutumin bai ganshi ido da ido ba, kuma saida ya dakatar da Cctv camera dake ta wajen get kana ya aiwatar da k’udurinsa, don yasan dole za’ayi bincike. Inada yak’inin baiyi hakan ba saida ya samu goyon bayan manyanmu don kuwa karan kanshi bazai iya aikata hakan ba ba’a kamashi ba. don haka karka damu nasan yanda zan b’ullowa lamarin”.

Kuzeem ta fad’ama Bilal tana sakin wani guntun murmushi. Kai Bilal ya girgiza cike da gamsuwa da abinda ta fad’a, don kuwa dukkan wata yardarsa tana ga Kuzeem. Daga haka ta fara shigar da bayanan da ta shirya a cikin Computer da ke gabanta, yayinda Bilal ya d’an rank’wafo yana kallon yanda take sarrafa fararen yatsunta a kan keyboards d’in Computer cike da k’warewa, don kuwa Kuzeem ta iya sarrafa Computer fiye da zaton mai karatu. Saida ta gama sannan ta mik’e suka fice daga wurin.

Wata irin razanannar mik’ewa Major Khalil yayi ganin Kuzeem tsaye cikin office d’inshi.✍️

✨Thanks for reading my story✨

#Anup?³⁶ ⁴⁰

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) - AREWAINFO NOVELS (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Ray Christiansen

Last Updated:

Views: 5501

Rating: 4.9 / 5 (49 voted)

Reviews: 88% of readers found this page helpful

Author information

Name: Ray Christiansen

Birthday: 1998-05-04

Address: Apt. 814 34339 Sauer Islands, Hirtheville, GA 02446-8771

Phone: +337636892828

Job: Lead Hospitality Designer

Hobby: Urban exploration, Tai chi, Lockpicking, Fashion, Gunsmithing, Pottery, Geocaching

Introduction: My name is Ray Christiansen, I am a fair, good, cute, gentle, vast, glamorous, excited person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.